Kamar Murtala kamar Buhari, `yan kasa a taimaka wa Buhari
A ranar Asabar din makon jiya ce 13-02-2015, aka kawo karshen tarurruka da addu`o`in zagayowar ranar da aka kasha tsohon shugaban kasa Janar Murtala Ramat Mohammed, a cikin wani juyin mulkin da bai yi nasara ba. Ranar ta bana ta kasance ita ce ta cika shekaru 40 cif-cif, wato 13-02-1976, da wancan juyin mulki da […]
A ranar Asabar din makon jiya ce 13-02-2015, aka kawo karshen tarurruka da addu`o`in zagayowar ranar da aka kasha tsohon shugaban kasa Janar Murtala Ramat Mohammed, a cikin wani juyin mulkin da bai yi nasara ba. Ranar ta bana ta kasance ita ce ta cika shekaru 40 cif-cif, wato 13-02-1976, da wancan juyin mulki da aka yi a Legas a daidai lokacin da ake tafiya da shi zuwa ofis. Juyin mulkin da wasu sojoji suka yi yunkurinsa a karkashin jagorancin Laftanar Kanar Bukar Suka Dimka. Ka iya cewa, bayan kasancewar zagayowar ranar daidai da cika shekaru 40 da kisan gillar, kasancewar kuma Shugaba Muhammadu Buhari yana kan karagar mulki, ya kara mata armashi. Don Shugaba Buharin ya yi gwamnan rusashshiyar Jihar Arewa maso Gabas ta wancan lokacin mai Hedkwata a Barno (tsohuwar jihar da a yau ta kunshi shiyyar Arewa maso Gabas mai jihohi shidda, wato Borno da Gwambe da Yobe da Taraba da Adamawa da Bauchi). Kazalika Shugaba Buharin tun bayan da ya zo kan karagar mulki, yau watanni takwas, babban abin da ya sa gaba, shi ne, yaki da cin hanci da rashawa, da kokarin saita alkiblar kasar nan da mutanenta a kan a dawo kan zaman gaskiya, a tsare amanar talakawa a kuma girmama juna kamar dai yadda Murtala ya fara yi a cikin mulkinsa na kwanaki 199.
A cikin tarurruka da addu`o`in da aka yi akwai jagorantar Sallar Juma`a da mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na II, ya yi a Masallacin Murtala da ke kewayen birinin Kano, tare da yin addu`o`i, bayan idar da Sallar a bakin kabarin marigayin da ke cikin harabar Masallacin sannan aka karkare da gagarumar lacca a Otel Transcorp Hilton da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Asabar din da ta gabata.
Gidauniyar Murtala Mohammed, Gidauniyar da babbar diyar marigayin Uwargida A`isha Mohammed Oyebode, take shugabanta, ita ta shirya tarurrukan da addu`o`in.
A cikin hudubar waccan Sallar Juma`a, mai Martaba San Kano ya bayyana cewa, babban abin da ya sa a kullum ake tunawa da tsohon shugaban kasa Janar Murtala, bai wuce saboda irin kisan gillar da aka yi masa ba, a kan bai jib a, bai gani ba, da kuma ayyukan alherin da ya shimfada wa kasar nan a cikin dan wa`adin mulkinsa na kwanaki kadan. A nan sai ya yi fatan shgabanni da sauran `yan kasa za su rinka koyi da halaye nagari na tsohon shugaban kasar.
Shi ma da yake nasa jawabin a waccan kasaitacciyar lacca, shugaba, cewa ya yi, kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban kasa Janar Murtala, ya yi matukar mayar da kasar da al`ummar baya a cikin karfaffan ginshikin da ya so ya dora ta, bisa ga yadda ya same ta kusan kome a lalace, ga cin hanci da rashawa da rashin da`a sun yi katutu a zukatan al`umma. Dukkan wadancan, miyagun dabi`u, in ji Shugaba Buhari, Janar Murtala ya himmatu wajen yakarsu, tare da kokarin kafa harsashin inda kasar nan za ta fuskanta a zaman kasa mai tinkaho da kanta. A nan Shugaba Buhari, ya yi fatan dukkan `yan kasa da su yi koyi da halayen tsohon Shugaban kasa Janar Murtala na kamanta gaskiya da rikon amana da biyayya da da`a.
Yanzu bari mu duba wasu daga cikin irin ayyukan alherin da Janar Murtala ya yi da har shugabanni da talakawa suke ta yabonsa, yau shekaru 40, bayan ba shi. Janar Murtala ya kwace mulki ne daga hannun Janar Yakubu Gowon, bayan Janar Gowon din ya kwashe shekaru tara yana mulki 1967 zuwa 1975, babu kuma wata alama zai mika mulkin hannun farar hula kamar yadda ya yi ta alkawarin zai yi. A wancan lokaci bayan kin mika mulki ga hannun farar hula akwai kuma koken a kara kirkiro jihohi da taso da Hedkwatar kasar nan daga Legas zuwa wani wuri da ya fi dacewa da sukurkucewar ayyukan gwamnati da babbar annobar cin hanci da rashawar da kasa ba ba a taba gani ba a cikin tafiyar da ayyukan gwamnatoci da dai sauran matsalolin.
Zuwan Janar Murtala da mataimakansa ke da wuya, suka shiga aiki ba ji ba gani, ba dare ba rana, inda ya tabbatar da kafa Kwamitin da ya rubuta sabon daftarin tsarin mulkin kasar nan na 1979, a karkashin babban lauyan nan Cif Rotimi Williams, wanda samar da wannan daftari ne ya kai fagen da Gwamnatin Janar Olusegun Obasanjo da ya gaji Janar Murtala ta shirya zabubbukan 1979, ta kuma mika mulki ga gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari na Jam`iyyar NPN a ranar 1-10-1979, a bisa ga tsarin shugaba mai cikakken iko irin na kasar Amurka. Gwamnatin Janar Murtala/Obasonjo ce ta yanke hukuncin dawo da Hedkwatar kasar nan daga Legas zuwa Abuja, sannan shi ne ya kirkiro karin jihohi bakwai na Neja da Gongola da Ondo da Imo da Binuwai da Ogun da Bauchi, daga 12 suka zama 19, a ranar 3-02-1976, kwanaki 10 kafin a yi masa kisan gilla.
Gwamnatin Janar Murtala ce ta fara tankade da rairayar korar ma`aikatan gwamnatoci, har su dubu 10, bisa ga zargin yin sakaci da aiki ko cin hanci da rashawa ko rashin lafiya, sannan ta kori dukkan gwamnonin mulkin soja na jihohi 12 da suka hada da Kantoman mulkin na Jihar Gabas, daga bisani kuma kwamitin binciken da ta kafa musu ya samu dukkansu in banda biyu da laifuffukan wawure dukiyoyin al`umma, al`amarin da ya sa aka kwace dukiyoyinsu da na makarrabansu, irin su Ministoci da Kwamishinoni da manya-manyan Sakatarori, bayan an yi musu ritayar dole. Gwamnatin Murtala ce ta yi ritayar dukkan wani hafsan soja da ya haura mukamin Birgediya a lokacin.
A cikin gyare-gyaren Hukumomin gwamnati da sunan kasa ta zama daya, ya sanya Janar Murtala ya rushe Hukumomin gudanar da wasu Hukumomi da ma`aikatu na tsofaffin lardunan Arewa da na Gabashin kasar, ya mayar da Hukumomin da suke karkashinsu, irin su Kamfanin Buga Jaridun New Nigerian da Gidajen Radiyo da Tebejin na Kaduna da na Enugu da Legas da Jami`ar Ahmadu Bello da ke Zariya ga hannun gwamnatin tarayya, sannan gwamnatinsa ta karbi kashi 60 cikin 100 na hannun jarin Kamfanin buga jaridun Daily Times da ke Legas. Gwamnatin Murtala ce ta fara kirkiro Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ya danka shugabancinta ga shahararren dan jaridan nan Alhaji Babatunde Jose, Hukumar daga ita ce Shugaba Obasanjo a dawowarsa mulki karo na biyu ya kirkiro Hukumomi irin na EFCC da ICPC da kotun da`ar ma`aikata ta CCBT.
Mai karatu kadan ke nan daga cikin ayyukan alherin mulkin Janar Murtala, wanda tun bayan kisansa, ba a samu gyauron gwamnatinsa ba, sai da Shugaba Janar Muhammadu Buhari ya yi wa gwamnatin farar hula ta Alhaji Shagari juyin mulki a shekarar 1984, gwamnatin da ya tarar cike da matsaloli irin na cin hanci da rashawa da tabarbarewar ayyukan gwamnati da makamantansu, kwatankwacin irin wadanda Janar Murtala ya tarar.
A wancan lokacin Janar Buhari ya yi kokarin gyara wadancan barnace-barnace a cikin watanni 20 da gwamnatinsa ta yi. Amma shugabancin da ya yi masa juyin mulkin a shekarar 1985, shi gwamnatinsa ta mayar da hannun agogo baya, ta hanyar yafe wa mutanen da suka yi waccan barna tare da mayar musu kaddarorinsu da gwamnatocin Janar Murtala da Janar Buhari suka kwace, aka koma `yar gidan jiya.
Haka tarihin tafiyar da kasar nan ya tabbatar zuwa yanzu, to, kamata ya yi tunda yanzu Gwamnatin Shugaba Buhari da ya dawo ta hanyar mulkin dimokuradiyya ta tarar da barnar da ta fi ta baya, kuma ta dukufa wajen ganin ta maganceta, ya zama wajibi kowa ya kama wa Gwamnatin Shugaba Bahari, don kuwa kamar Murtala kamar Buhari.