Kamaru ta cafke mutane 3 da ke da alaka da Boko Haram
A wani samame da jami’an tsaron kasar Kamaru suka kai garin Goulfey mai makwabtaka da kasar Chadi, sun yi sa’ar cafke mutane uku wadanda ake kyautata zaton suna da alaka da kungiyar nan ta Boko Haram. An kama mutanan ne sakamakon wasu makamai da aka same su da su a lokacin da suke kokarin shiga […]
A wani samame da jami’an tsaron kasar Kamaru suka kai garin Goulfey mai makwabtaka da kasar Chadi, sun yi sa’ar cafke mutane uku wadanda ake kyautata zaton suna da alaka da kungiyar nan ta Boko Haram.
An kama mutanan ne sakamakon wasu makamai da aka same su da su a lokacin da suke kokarin shiga Kamaru daga iyakarta ta Chadi, a halin yanzu dai mutanen na ci gaba da kasance wa a tsare don gudanar don ci gaba da bincike.
Dalili da irin wannan barazanar tsaron ne, gwamnatin Kamaru ta bayyana karin daukar matakan karfafa tsaro a fadin kasar. A fatan ta na ganin cewa yankin Arewacin kasar bai zama wani sansani na ‘yan ta’adda ba, wadanda ke yin amfani da yankin domin tada zaune tsaye a kasashe makwabta. A cewar hukumonin kasar babban matsalar da kasar ke fuskanta shi ne na rashin katange mafi yawan iyakokinta da kasashe makwabta, sa’annan kuma garuruwa na nesa ne da iyakokin kasar lamarin da ke ba miyagu damar cin karensu ba babbaka.
kasashen Kamaru da Najeriya dai sun hada gwiwa domin yakar ayyukan ta’addaci da matsalar fashi-da-makami da kuma matsalar satar mutane.
Idan dai ba a manta ba a tsakiyar wannan watan ne, wasu suka yi garkuwa da wani basaraken garin Ngoumouldi-Kerawa da yaronsa a iyakar Kamaru da Jihar Barno. Bayan da kokarin kubutar da su ya ci tura, sai aka tsinci gawar Sarkin da ta yaron nasa a mace. Da aka duba gawarwakin sai aka fahimci cewa an yi masu yankan rago ne. Lamarin da daga bisani kuma aka dora alhakinsa ga kungiyar Boko Haram.