Kamaru ta cafke ’yan Boko Haram 3 a Maroua

A ranar litinin da ta gabata ne jami’an tsaro a garin Maroua da ke yankin arewacin kasar Kamaru suka kama mutane uku da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne.A cewar ministan cikin gidan kasar, Issa Chiroma Bakari, wadanda aka kaman, sun yi niyyar kai hare-hare ne a birnin.Ministan ya shaida wa gidan rediyon RFI […]

Kamaru ta cafke ’yan Boko Haram 3 a Maroua
Kamaru ta cafke ’yan Boko Haram 3 a Maroua

A ranar litinin da ta gabata ne jami’an tsaro a garin Maroua da ke yankin arewacin kasar Kamaru suka kama mutane uku da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne.
A cewar ministan cikin gidan kasar, Issa Chiroma Bakari, wadanda aka kaman, sun yi niyyar kai hare-hare ne a birnin.
Ministan ya shaida wa gidan rediyon RFI cewa wani dan acaba ne ya taimaka aka cafke mutanen, bayan ya fahimci cewa mutumin da ya dauka na nuna wasu halaye abin shakka, saboda haka maimakon ya sauke shi inda ya bukata, sai kawai ya nufi ofishin ‘yan sanda da shi, kuma nan take aka gano cewa mutumin dan Boko Haram wanda ke dauke da bama-bamai a jikinsa.
Ministan ya jinjina wa dan acabar domin ya taimaka wajen ceto rayukan jama’a, tare da taimakawa wajen gano ‘Yan Boko Haram.
Yanzu haka dai mahukunta a Kamaru na tsare da mutane uku da suka yi yunkurin kai harin kunar bakin wake a garin Maroua.