Kamaru ta dauki mataki kan cutar Ebola
Bullar kwayar cutar Ebola, wadda ta lakume rayukan jama’a a yankin Yammacin Afirka, ya sa hukumomi a Kamaru sun fara daukar mataki domin iyakance bazuwar cutar. A dalilin haka ne aka nemi ga jama’a da kuma kamfanonin safara na sama da na kasa da kuma na ruwa na kasashen Najeriya da Laberiya da Saliyo da […]
Bullar kwayar cutar Ebola, wadda ta lakume rayukan jama’a a yankin Yammacin Afirka, ya sa hukumomi a Kamaru sun fara daukar mataki domin iyakance bazuwar cutar.
A dalilin haka ne aka nemi ga jama’a da kuma kamfanonin safara na sama da na kasa da kuma na ruwa na kasashen Najeriya da Laberiya da Saliyo da kuma Guinea da su dakatar da yin kai-kawo zuwa kasashen da cutar ta bulla. Har ila yau Kamaru ta dakatar da duk wasu musayar kayayyakin haja da wadannan kasashen. Matakan farko da gwamnati ta dauka su ne bincikar lafiyar fasinjoji da suke shigowa daga Yammacin Afirka da kuma aika jami’an kiwon lafiya iyakokin kasa.
Hakan nan ma shigowar jama’an wadannan kasashe zuwa Kamaru an tsaida shi cik ta dukkanin hanyoyin fita da kuma shiga kasar. Duk wasu kamfanoni na safara da ke ya da zango, wannan dokar ta shafe su. A karshen makon jiya ne ma’aikatar sufuri da ta kiwon lafiya suka sa hannu a kan wannan hukunci. Kodayake ministan kiwon lafiya ya ce matakin na gajeren lokaci ne ba tare da kuma ya bayyana tsawon wa’adin ba.
Amma kuma Kakakin Gwamnati Minista Issa Chiroma Bakary ya ce hakan zai kwashi lokaci kwatakwancin tsawon wa’adi tsakanin harbuwa da kwayar cutar da take haddasa zazzzabin Ebola da kuma bayyanar alamun farko na cutar a jikin mutum. Ministan kuma ya ce wannan matakin yana da tsauri amma kuma zai amfanar da gaske wurin kare bazuwar cutar kamar yadda jama’a ke dinga kai kawo a tsakanin kasashen biyu. Sai dai kuma tuni hakan ya fara shafar rayuwar jama’a ’yan kasuwa da kuma masu wasu ma’amala daga nan izuwa can. Masana tattalin arziki sun bayyana cewa kasar Kamaru ita ce babbar kasa wurin yin musayar kayan haja da Najeriya.