Kamaru ta fara kai wa Boko Haram hari ta sama
A karshen makon jiya ne ’yan kungiyar Boko Haram suka zafafa kai hare-harensu a wasu garuruwa biyar da suke kan iyakokin Kamaru da Najeriya kamar su Mokolo, Guirbidig, Waza, Amchide da kuma Makary. Na baya-bayannan shi ne harin da suka kai garin Ashigashiya, inda rahotanni suka ce yawan ’yan kungiyar Boko Haram din ya kama […]
A karshen makon jiya ne ’yan kungiyar Boko Haram suka zafafa kai hare-harensu a wasu garuruwa biyar da suke kan iyakokin Kamaru da Najeriya kamar su Mokolo, Guirbidig, Waza, Amchide da kuma Makary.
Na baya-bayannan shi ne harin da suka kai garin Ashigashiya, inda rahotanni suka ce yawan ’yan kungiyar Boko Haram din ya kama kusan dubu daya. Rahotanni daga majiyoyi daban-daban na tabbatar da cewa akalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu a wannan musayar harbe-harbe da ya wakana a tsakanin ’yan kungiyar da dakarun gwamnatin Kamaru. Rahotannin wadanda ba na gwamnatin ba ne na cewa an yi asarar rayukan jama’a fararen hula da kuma wasu sojoji hudu hadi da ’yan kungiyar Boko Haram sama da 30 a yunkurin da dakarun na Kamaru suka yi wurin fatattakar ’yan kungiyar wadanda suka kafa tutarsu a garin Ashigashiya. Kodayake, hakan na gajeren lokaci ne. Amma kuma sanarwar da kakakin Gwamnatin kasar Minista Issa Tchiroma Bakary ya fitar a ranar Litinin, ya tabbatar da wani bangare na majiyoyin farko wadanda suka ce kusan ’yan kungiyar dubu daya ne suka fito suka fafata da dakarun Gwamnati a wasu garuruwa na kan iyaka masamman ma a garin Ashigashiya.
Har ila yau, dakarun sun yi amfani a karon farko da jiragen sama wurin mayar da martani ga Boko Haram. Amma Mista Bakary ya ce, za a samu bayanan abin da ya gudana bayan an kammala gudanar da bincike. Abin da ya danganci sauran hare-haren da suka gudana a sauran garuruwa na kan iyaka irin su Limani da Makary, inda dakarun gwamnati suka hallaka ’yan kungiyar 34 suka kuma kwashe wasu motoci da ke hannunsu, a yayin da kuma soja guda daga bangaren dakarun gwamnati ya rasa ransa. Hakannan shi ma Laftanal Kanar Didier Badjeck mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ya ce, sun fahimci cewa a yanzu haka kungiyar Boko Haram na yunkurin dabaibayesu baki daya. Saboda haka ya ga cewa yin amfani da jiragen sama wurin yakarsu yana da amfani a dalilin cewa hakan zai ba da daman sassauta yawan kai-kawo da kuma sawaka musu ayyuka. Ya ce: “Tun farko mun ji tsoron yin amfani da jiragen saman yaki saboda muna shakkun cewa hakan ka iya jawo asarar da ba za a iya kimantawa ba. Amma kuma har idan muka samu tantance wurin da abokan gaba suke, babu shakka yin amfani da jiragen sama shi ya dace,” inji shi.
Dangane da irin lamarin da Boko Haram take haddasawa a arewacin Kamaru, shi kuma Samuel Kleda, babban limamin cocin mabiya darikar Katolika a birnin Douala, ya ce zai yi wuya da a danganta wannan rubanya kai hare-haren da ’yan kungiyar Boko Haram suke yi da batun addini. Saboda kamar yadda ’yan kungiyar suke kashe Musulmi, hakazalika nan suke kashe mabiya addinin Kirista. Kenan abin da suke yi yana da dangantaka da siyasa.
Har ila yau, hare-haren da kungiyar Boko Haram take kaiwa a jere ya jefa jama’a mazauna kan iyakar da Najeriya cikin wani mawuyacin hali, inda da dama suka fara kaurace wa muhallansu domin neman sabbin mafaka.