‘Kamaru ta kashe ‘yan Boko Haram 100’

Mahukunta a Kamaru sun bayyana cewa dakarun kasar sun kashe ‘yan kungiyar Boko Haram fiye da 100 a lokacin da mayakan kungiyar ke kokarin kutsawa cikin kasar.A ranar Litinin da ta gabata ne kakakin gwamnatin Kamaru Issa Tchiroma Bakary, ya fitar da wata sanarwa ta gidan rediyo, inda ya ce a ranar Asabar ‘yan kungiyar […]

‘Kamaru ta kashe ‘yan Boko Haram 100’
‘Kamaru ta kashe ‘yan Boko Haram 100’

Mahukunta a Kamaru sun bayyana cewa dakarun kasar sun kashe ‘yan kungiyar Boko Haram fiye da 100 a lokacin da mayakan kungiyar ke kokarin kutsawa cikin kasar.
A ranar Litinin da ta gabata ne kakakin gwamnatin Kamaru Issa Tchiroma Bakary, ya fitar da wata sanarwa ta gidan rediyo, inda ya ce a ranar Asabar ‘yan kungiyar sun harba makaman roka daga garin Fotokol da ke lardin Arewa-Mai-Nisa, abinda ya sa sojojin Kamaru suka maida martani har mayakan Boko Haram fiye da 100 suka mutu. Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirarin. Kuma babu rahoton asarar rai ko jikkata daga bangaren dakarun Kamarun, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana.
Hakazalika, gwamnatin Kamaru a wani mataki na kyautata tsaron yankin ta sanar da rufe wasu makarantu da ke lardin.
Tun bayan da ‘yan Boko Haram suka kwace garin Gamborou Ngala da ke iyakar Najeriya da Kamaru, dubban ’yan gudun hijira ne suke shiga kasar don neman mafaka daga tashin hankalin.
Har ila yau, a shekaranjiya Laraba ne, al’ummar da ke zaune a yankin  Bakassi, wanda shi ma yake kan iyaka da Kamaru, suka kauracewa muhallansu saboda hare-haren da dakarun Kamaru ke kai masu, kamar yadda suka bayyana.
A shekarar 2008 ne aka cimma wata yarjejeniya mika yankin zuwa ga Kamaru. Kodayake, jama’ar yankin sun ci gaba da kalubalantar matakin wanda kuma hakan ke haifar da barazanar tsaro a yankin mai arzikin man fetur.