Kamaru ta kori sojojinta 2 don sakaci a yaki da Boko Haram
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya sallami wasu manyan hafsoshin sojin kasar biyu da ke yankin arewa mai nisa bayan wani harin ’yan kungiyar Boko Haram wanda ya yi sanadiyya mutuwar mutum bakwai da kuma sace mai dakin mataimakin firaministan kasar, Amadou Ali.A ranar Lahadin da ta gabata ne ’yan Boko Haram suka yi awon […]
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya sallami wasu manyan hafsoshin sojin kasar biyu da ke yankin arewa mai nisa bayan wani harin ’yan kungiyar Boko Haram wanda ya yi sanadiyya mutuwar mutum bakwai da kuma sace mai dakin mataimakin firaministan kasar, Amadou Ali.
A ranar Lahadin da ta gabata ne ’yan Boko Haram suka yi awon gaba da matar a garin Kolofata da ke makwabtaka da Najeriya. Akalla dai sojoji biyu ne suka mutu sakamakon harin.
A karkashin wata doka da aka sanar ta gidajen rediyon kasar, ta bayyana dakatar da Kanal Youssa Gedeon da Kanal Justin Ngonga kwamandoji da ke jagorantar bataliya daya kowane a yankin arewacin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.
Wadannan ne dai hafsoshin sojin kasar da ke jagorantar yaki da Boko Haram a yankin. Gwamnatin Najeriya ta ce ’yan ta’addan na amfani da ita a matsayi wani sansani na bayan gida.
A wani mataki na shawo kan wannan barazanar ne, Gwamnatin Kamaru ta bullo da wasu matakai don inganta tsaro akan iyakokinta da Najeriya, inda ta aike da soji guda 1,000 wadanda kasancewarsu a wurin bai hana kai harin ba.
Kodayake, a ranar Litinin da ta gabata aka samu labarin kubutar da uwar gidan firaministan da aka sace. Amma a ranar Talata sashin Hausa na BBC ya ruwaito cewa akwai shakku a labarin kubutar da wadanda ’yan Boko Haram din suka yi garkuwa da su.