Kamaru ta yi na’am da kafa rundunar tsaro a tafkin Chadi
Tabarbarewar tsaro da ake fuskanta a kasashen da ke makwabtaka da kasar Kamaru ya tilasta wa kasar shiga Rundunar Tsaron yankin Chadi a fatanta na ganin an kara kyautata tsaron yankin.Matakin na Gwamnatin Kamaru ya biyo bayan kammala taron ministocin tsaro na kasashen Hukumar Raya tafkin Chadi(Karo na biyu) da aka yi a birnin Yaounde […]
Tabarbarewar tsaro da ake fuskanta a kasashen da ke makwabtaka da kasar Kamaru ya tilasta wa kasar shiga Rundunar Tsaron yankin Chadi a fatanta na ganin an kara kyautata tsaron yankin.
Matakin na Gwamnatin Kamaru ya biyo bayan kammala taron ministocin tsaro na kasashen Hukumar Raya tafkin Chadi(Karo na biyu) da aka yi a birnin Yaounde ranar Talatar da ta gabata. kasashen da ke cikin hukumar dai sun hada da Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da Libya da kuma Jamhuriyar Tsakiyar Afirka. Taron dai an fara shi ne a shekarar 2012 a kasar Nijar.
Ministan Tsaron Kamaru Edgard Alain Mebe Ngo’o ya bayyana cikakken goyon bayan kasarsa ga rundunar kuma ya ce Kamaru zata ba da gudunmawar sojoji 700, kuma ya ba da tabbacin biyan duka kudaden bashin da hukumar ke binta.