Kamfani ya bai wa ma’aikata gwale-gwale saboda rashin cika alkawari

A ranar 14 ga Janairun bana ne wani kamfani da ke Lardin Shandong a kasar China, ya bai wa shida daga cikin ma’aikatansa gwale-gwale saboda gaza cika alkawarin da suka yi don sayar da hajar kamfanin. An dai ba su gwale-gwalen ne ta hanyar tafiya a kan hannuwa da gwiwoyinsu wato rarrafe a titunan garin. Wannan […]

Kamfani ya bai wa ma’aikata gwale-gwale saboda rashin cika alkawari

A ranar 14 ga Janairun bana ne wani kamfani da ke Lardin Shandong a kasar China, ya bai wa shida daga cikin ma’aikatansa gwale-gwale saboda gaza cika alkawarin da suka yi don sayar da hajar kamfanin. An dai ba su gwale-gwalen ne ta hanyar tafiya a kan hannuwa da gwiwoyinsu wato rarrafe a titunan garin.

Wannan abin kunyar da aka sanya ma’aikatan kamfanin a ciki ya faru ne a birnin Zaozhuang yayin da masu wucewa suke kallon abin a matsayin cin mutuncin ma’aikatan, ganin yadda ma’aikata shida suke tafiya da gwiwoyinsu a cikin cinkoson motoci da ke wucewa a titunan. Akwai daya daga cikin ma’aikatan kamfanin dauke da jar tuta wanda aka rubuta sunan kamfanin. Su dai wadannan ma’aikata da aka ba gwale-gwalen ba a ba su wani abu da zai kare lafiyar jikinsu ba, sai dai kawai kayan da suke zuwa ofishinsu da su. Duk da haka ma’aikatan sun kiyaye umarnin kamfanin don ladabtar da su, saboda gudun rasa ayyukansu a kamfanin.

Masu wucewa ta hanyar sun sanar sa ’yan sanda lamarin ganin yadda ake ta yi wa ma’aikatan gwale-gwale. Wata kafar sadarwa ta China ta fitar da rahoton cewa, an dakatar da kamfanin na wani lokaci don yin bincike kan sanadin bai wa ma’aikatan gwale-gwale.

An yi ta sukar kamfanin a shafukan muhawara na Intanet sakamakon bidiyon da aka yada na ma’aikatan suna gwale-gwalen a layukan garin Zaozhuang. Daya daga cikin manajojin kamfanin ya ce, wannan gwale-gwalen da aka sa ma’aikatan zai kara wa sauran ma’aikata kwazo wajen tabbatar da sun yi kokarin cika alkawarin da suka dauka na sayar da hajar kamfanin.

Ana zargin kamfanonin kasar China da yi wa ma’aikatansu gwale-gwale musamman wadanda suka gaza gudanar da ayyukansu. A shekarar da ta gabata ce aka fitar da rahoton yi wa wadansu ma’aikatan wani kamfani horo da cin kyankyaso a garin Zunyi na kasar China saboda gaza cimma muradun kamfanin.

Ambaliya: Binani ta bai wa Maiduguri tallafin 50m

An sallami sojar da ta zargi shugabanta da neman lalata da ita

CBN ya ƙara kason kuɗin ruwa zuwa 27.25 cikin 100

Hatsarin kwalekwale ya ci rayuka 4 a Borno