Kamfanin Adidas ya daina hulda da dan tseren Amurka Tyson Gay

A ranar Litinin da ta gabata ne, shahararren kamfanin da ke samar da kayayyakin wasanni da ke Jamus mai suna Adidas ya bayyana cewa tuni ya raba-gari da dan tseren Amurka Tyson Gay saboda zargin da ake masa na yin tu’ammali da kwayoyin da ke sanya kuzari a lokacin da ake gasar tsere.Shi dai Tyson […]

Kamfanin Adidas ya daina hulda da dan tseren Amurka Tyson Gay
Kamfanin Adidas ya daina hulda da dan tseren Amurka Tyson Gay

A ranar Litinin da ta gabata ne, shahararren kamfanin da ke samar da kayayyakin wasanni da ke Jamus mai suna Adidas ya bayyana cewa tuni ya raba-gari da dan tseren Amurka Tyson Gay saboda zargin da ake masa na yin tu’ammali da kwayoyin da ke sanya kuzari a lokacin da ake gasar tsere.
Shi dai Tyson Gay, hukumar da ke gwada ’yan tsere ta duniya ta same shi da laifin yin amfani da kwaya mai sanya kuzari ne a gasar da ta gudana a watan Mayun wannan shekara.
Jim kadan da bayyana masa sakamakon gwajin ne dan tseren ya yanke shawarar ficewa daga gasar tseren da za ta gudana a wata mai zuwa a Mosko da ke kasar Rasha.
“Mun kadu matuka da sakamakon gwajin da aka yi wa dan tseren da muke huldar azriki da shi don haka muka yanke shawarar dakatar da shi har sai abin da hali ya yi”, inji sanarwar da kamfanin Adidas ya fitar.
“Dokarmu ta nuna za mu yanke hulda da duk wanda muka kulla yarjejeniya da shi amma aka same shi da laifin yin magudi saboda haka wannan hukunci da muka yanke a kan Gay abu ne da ke bisa ka’ida”.
dan kimanin shekara 30, Tyson Gay ya fara huldar arziki da kamfanin Adidas ne tun cikin shekarar 2005.
Rahotanni sun tabbatar dan tseren zai rasa miliyoyin Daloli bayan da kamfanin Adidas ya daina hulda da shi kuma ana kyautata zaton kamfanoni da dama za su janye da yin hulda da shi saboda matsalar da ya fada.
Tyson Gay yana daga cikin ’yan tseren Amurka da take ji da su a gasar tsere ta duniya da kuma ta Olamfik.