Kamfanin AEDC ya kafa kwamitin mutum shida kan hadarin wutar Neja
Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Abuja wanda a takaice ake kira (AEDC) ya ce ya kafa kwamitin bincike na mutum shida don ya binciki abinda ya haddasa hadarin wutar day a auku a ranar Asabar din da ta gabata a Unguwar Biri kusa da garin Mina da ke jihar Neja. Wata takardar sanarwa da Shugaban […]

Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Abuja wanda a takaice ake kira (AEDC) ya ce ya kafa kwamitin bincike na mutum shida don ya binciki abinda ya haddasa hadarin wutar day a auku a ranar Asabar din da ta gabata a Unguwar Biri kusa da garin Mina da ke jihar Neja.
Wata takardar sanarwa da Shugaban Sashen Hulda da Jama’a da Manema Labarai, Ahmed Shekarau ya raba wa manema labarai, ta nuna cewa rahoton binciken farko na hadarin, ya nuna cewa wayar da ke dauke da layin wutar KV 11ce ta cire, sakamakon guguwar iska, ta hade da jar wayar da ke dauke da KV 415, sai hakan ya janyo karfin wutar ya karu har ya hallaka mutum biyu wasu kuma suka ji rauni.
Da yake kaddamar da kwamitin jiya a Abuja, Daraktan Hadari da Bin Ka’ida na kamfanin, Injiniya Collins Chabuka ya yi watsi da jita-jitar da ke yawo cewa hadarin wutar ya shafi gidaje 49.
“Ya na daga cikin ka’idojin kare lafiya na kamfanin (AEDC) cewa duk hadarin da ya auku, ma’aikatan da ke da kwarewa da kuma sanin yadda masana’antar wutar lantarki take, su ne za su binciki lamarin. Dalilin binciken shi ne a gano matsalolin da suka haddasa hadarin tare da bayar da shawara kan matakan da za a dauka don kare sake aukuwar lamarin nan gaba”. Inji shi.
Ya bayyana hadarin da wani abin kaico tare da bayar ta tabbacin cewa kamfanin (AEDC) ya bi dukkan ka’idojin da Ma’aikatar da ke sanya ido ga kamfanonin wutar lantarki (NERC) da kuma Ma’aikatar da ke lura da yadda ake amfanin da wutar lantarki ta (NEMSA) suka gindaya.