Kamfanin Aminiya da Gwamnatin Kano za su gudanar da taro kan illar shan miyagun kwayoyi
Kamfanin Media Trust da ke buga jaridun Daily Trust da Aminiya da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Kano ya shirya gangamin wayar da kan jama’a kan illar shan miyagun kwayoyi a jihar. Da yake yi wa Aminiya karin bayani, Manajan Shirya Taro da Shagulgula na kamfanin Media Trust, Abdurrahman Usaini, ya ce kamfanin ya shirya taron […]
Kamfanin Media Trust da ke buga jaridun Daily Trust da Aminiya da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Kano ya shirya gangamin wayar da kan jama’a kan illar shan miyagun kwayoyi a jihar.
Da yake yi wa Aminiya karin bayani, Manajan Shirya Taro da Shagulgula na kamfanin Media Trust, Abdurrahman Usaini, ya ce kamfanin ya shirya taron ne don wayar da kan jama’a kan illar shaye-shaye a jihar da sauran jihohin Arewacin Najeriya.
“Mun lura da yadda shan miyagun kwayoyi ke kara ta’azzara, saboda haka muka shirya taron da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Kano don mu wayar da kan jama’a bisa illar shan miyagun kwayoyi a tsakanin al’umma,”. Inji shi.
Ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano tuni ta amince ta hada gwiwa da kamfanin don gudanar da taron wanda zai yi maganin illar shan miliyoyin kwayoyi a jihar.
Usaini ya bayyana cewa kwararru daban-daban za su yi jawabi ga dimbin matasa kan illar shan miyagun kwayoyi a taron. Ya ce taron zai gudana daga ranar 15 zuwa 16 ga Watan Nuwamban shekarar da muke ciki a Jihar Kano.
Ya kara da cewa ranar 15 ga wata mutum kimanin 200 sanye da rigunan da ke fadakarwa kan illar shan miyagun kwayoyi za su yi tattaki zuwa fadar Sarkin Kano, inda Sarki zai yi jawabi a fadarsa.
Ya cigaba da cewa ranar 16 ga wata za a gudanar da babban taron, inda kwararru za su yi lacca kan illar shan miyagun kwayoyi. Haka kuma ya kara da cewa Hukumar Yaki da Jabun Magunguna ta NAFDAC da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar da Hukumar Hana Sha da Ta’ammuli da Miyagun Kwayoyi ta NDLEA da Kungiyoyin da ke yaki da shan miyagun kwayoyi za su hallara a taron.
Ya ce Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje zai yi jawabi a taron. Ya dage a kan cewa kamfanin Media Trust ya yi imanin cewa ta hanyar taron za a rage shan miyagun kwayoyi a jihar.
Ya ce da zarar an kammala taron na Kano za a gudanar da irinsa a Jihohin Adamawa da Yobe da Jigawa da Katsina da Kogi da Taraba da Barno da Gombe da Bauchi da sauran jihohin Najeriya baki daya.