Kamfanin Apple ya amince da dokokin bayar da bayanai
Kamfanin Apple ya ba kai bori ya hau, inda ya bai wa hukumomin kasar Amurka hadin kai wajen samun bayanan masu amfani da wayoyin kamfanin.kididdiga daga kamfanin ta nuna cewa a shekarar 2015, Apple ya ba da kaso 80 cikin 100 na bayanan abokan huldarsa ga hukumomin Amurka, idan aka kwatanta da kaso 55 a […]
Kamfanin Apple ya ba kai bori ya hau, inda ya bai wa hukumomin kasar Amurka hadin kai wajen samun bayanan masu amfani da wayoyin kamfanin.
kididdiga daga kamfanin ta nuna cewa a shekarar 2015, Apple ya ba da kaso 80 cikin 100 na bayanan abokan huldarsa ga hukumomin Amurka, idan aka kwatanta da kaso 55 a Ingila.
Wani masanin harkar tsaro ya ce abin “bakin ciki ne” ga hukumomin tabbatar da anbi dokoki sau da kafa.
Kamfanin Apple ya saki rahoto ranar Litini kan bayanan da ya bayar tun daga shekarar 2013. Apple ya buga lambobin bayanan wayoyin da hukumomin tsaro suka nema.
Hukumomi suna zargin ana amfani da wayar iPhone wajen aikata laifuka.
Kamfanin ya kuma saki jerin bayanan da ma’aikatu suka nema da suka hada na iTunes da iCloud. Cikin kasashe biyar da suka fi mikawa Apple bukatar neman bayanai, da suka kai 2,000 a kowace shekara, Amurka ce kawai kasar da take samun hadin kan kamfanin a kusan kodayaushe, kamar yadda BBC ta bayyana.
Kasar Singapore ce ta zamo kurar baya a kusan kowace shekara. Kuma Amurka da Ingila ne suka kasance kasashen da suke neman bayanan mutane fiye da 300 a kowace shekara.