Kamfanin Apple ya kulla yarjejeniya da kamfanin China

Kamfanin Apple na Amurka ya kulla yarjejeniyar sayar da wayar iPhone ta hannun kamfanin wayar salula na China Mobile, wanda shi ne ya fi kowanne girma a duniya.Kamfanin China Mobile na da abokan hulda fiye da miliyan 760 kuma yana cikin kamfanonin China uku da aka bai wa lasisin samar da intanet samfurin 4G.Kamfanin Apple […]

Kamfanin Apple ya kulla yarjejeniya da kamfanin China
Kamfanin Apple ya kulla yarjejeniya da kamfanin China

Kamfanin Apple na Amurka ya kulla yarjejeniyar sayar da wayar iPhone ta hannun kamfanin wayar salula na China Mobile, wanda shi ne ya fi kowanne girma a duniya.
Kamfanin China Mobile na da abokan hulda fiye da miliyan 760 kuma yana cikin kamfanonin China uku da aka bai wa lasisin samar da intanet samfurin 4G.
Kamfanin Apple yana kokarin habaka cinikinsa a China, wacce ta zarta kasashen duniya wurin amfani da wayoyin komai-da-ruwanka, amma yana gwagwagwa da sauran kamfanonin kera wayoyin.
Fiye da mutane biliyan 1 da dubu dari biyu ne suke amfani da wayoyin komai-da-ruwanka a China amma cinikin iPhone ya ja baya sanadiyyar karbuwar wayoyi masu arha irinsu Samsung da Lenobo da Coolpad.
Kasuwar Apple ta yi kasa ne saboda sabanin kasashen da suka ci gaba, domin a kasashe masu tasowa kamfanin wayar salula ba sa rage kudin wayoyin komai-da-ruwanka.
Hakan na nufin wajibi ne masu saye su biya kudin wayar nan take, abin da ke sa kayan kamfanin Apple ke yi wa mutane tsada.
Domin shawo kan matsalar ne kamfanin Apple ya fitar da samfurin iPhone 5c mai arha a farkon shekarar nan.
 Manazarta sun ce saukaka farashin wayar tare da hada kai da kamfanin wayar salula mafi girma a duniya babbar dama ce ta bunkasa cinikin Apple.
Kamfanin Cantor Fitzgerald ya kiyasta cewa kamfanin  Apple na iya sayar da wayoyin iPhone miliyan 24 ga abokan huldar China Mobile kadai a badi.
A watanni tara na farkon shekarar nan dai Apple ya sayar da wayoyin iPhone miliyan 102 da dubu dari hudu ne.
Daga 17 ga watan Janairu ne masu layin China Mobile za su fara amfani da wayoyin iPhone 5s da 5c.