Kamfanin Ashaka ya sake wa kauyuka uku matsuguni

Kamfanin Siminti na Ashaka da ke Jihar Gombe ya sake tsugunar da wasu kauyuka uku wato Lariski da Darumpa da Malari inda aka gina musu gidajen zamani a kauyen Ladde Bage.Da yake jawabi a lokacin bikin mika gidajen ga al’ummar kauyuka shugaban kamfanin Mista Leo Palka, gode wa al’ummar Lariski da Darumpa da Malari ya […]

Kamfanin Ashaka ya sake wa kauyuka uku matsuguni
Kamfanin Ashaka ya sake wa kauyuka uku matsuguni

Kamfanin Siminti na Ashaka da ke Jihar Gombe ya sake tsugunar da wasu kauyuka uku wato Lariski da Darumpa da Malari inda aka gina musu gidajen zamani a kauyen Ladde Bage.
Da yake jawabi a lokacin bikin mika gidajen ga al’ummar kauyuka shugaban kamfanin Mista Leo Palka, gode wa al’ummar Lariski da Darumpa da Malari ya yi, bisa hadin kan da suka ba su wajen canja musu matsugunni daga inda suke zuwa kauyen Ladde Bage.
Mista Leo Palka, ya ce an gidajen da inganci kuma na bulo ba na kara da suke a ciki a da ba.
Shi kuwa Manajan Ayyuka na Kamfanin Injiniya Abdulhameed Balarabe, cewa ya yi kamfanin Simintin na Ashaka ya sauya wa al’umomin matsugunni ne zuwa kauyen Ladde Bage, saboda ya sami damar hakar ma’adinan da suka samu a wurin.
Injiniya Balarabe, ya ce an gina wa al’ummar gidaje 55 da Makarantar Firamare da asibiti da Masallaci da rijijojin burtsatse uku.
Shugaban Hukumar Daraktocin Kamfanin Alhaji Umaru Kwairanga, ya gode wa Allah bisa yadda suka dauki alkawari kuma suka cika wa al’ummomin. Alhaji Kwairanga, ya ce muddin al’ummomin suka ci gaba da ba su hadin kai da goyon baya wannan somin tabi ne na abubuwan da za su yi musu.
Wasu magidanta da suka ci gajiyar tallafin na Ashaka Alhaji Sarki Jibrin da Adamu Saleh, gode wa kamfanin Ashaka suka yi bisa wannan abin alheri da aka yi musu.
Sun roki gwamnatin Jihar Gombe ta samar musu da wutar lantarki da hanyar mota a wannan garuruwan nasu da kamfanin Ashaka ya gina musu.