Kamfanin Azman ya dakatar da dukkan ma’aikatansa

Ma’aikatan za su tafi hutu ba tare da albashi ba

Kamfanin Azman ya dakatar da dukkan ma’aikatansa

Jirgin Azman

Wata daya bayan ya dawo da zirga-zirga a Najeriya, kamfanin jiragen sama na Azman ya sake dakatar da aiki saboda karancin jiragen sama.

Kazalika, kamfanin ya kuma dakatar da dukkan ma’aikatansa, inda ya tura su hutun dole ba tare da albashi ba.

A cikin wata sanarwa da hukumar kamfanin ta fitar dauke da kwanan watan 3 ga watan Agusta, 2023, wacce mai kula da ma’aikata na kamfanin, Magaji Misau, ya sanya wa hannu, ta bukaci dukkan ma’aikatan da su tafi hutun sai wasu mutum takwas.

Wasikar ta ce, “idan zaku iya tunawa, mun dakatar da aiki a Najeriya saboda an kai jiragen bincike, kuma za a dauki tsawon lokaci kafin a kammala.

“A sakamakon haka, hukumar gudanarwar kamfanin ta umarci a sanar da shawarar da ta yanke cewa dukkan ma’aikata su tafi hutun dole ba tare da biyan albashi ba daga ranar daya ga watan Agusta 2023.”

A watan Satumban bara dai Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (NCAA) ta dakatar da kamfanin daga aiki a Najeriya saboda kin sabunta lasisinsa na AOC.

Lasisin dai ya kare ne tun a watanni uku na farkon shekara ta 2022.

 

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7