Kamfanin BF SUMA ya raba kyautar motoci ga dillansa

Kamfanin dillancin magunguna mai suna  BF SUMA ya raba kyautar motoci ga manyan dillalansa da suka yi fice wajen sayar da magungunansa a kasa baki daya. Da yake jawabi yayin bikin mika mukullun motocin uku ga dillalan wanda aka gudanar a Abuja a karshen makon da ya gabata, wakilin kamfanin a Najeriya, Mista Leo Wei, […]

Kamfanin BF SUMA ya raba kyautar motoci ga dillansa

Kamfanin dillancin magunguna mai suna  BF SUMA ya raba kyautar motoci ga manyan dillalansa da suka yi fice wajen sayar da magungunansa a kasa baki daya.

Da yake jawabi yayin bikin mika mukullun motocin uku ga dillalan wanda aka gudanar a Abuja a karshen makon da ya gabata, wakilin kamfanin a Najeriya, Mista Leo Wei, ya bayyana cewa kamfanin ya raba kyaututtukan ne don ya kara wa dillalansa kwarin gwiwa.

“Kamfaninmu kodayaushe yana la’akari da kokarin da kowane dillali yake yi. Saboda haka wannan shekarar ma muka yanke shawarar bayar da kayautar motoci ga daukacin dillalanmu da suka nuna bajinta a Najeriya,” inji shi.

Ya bayyana cewa a ’yan shekarun da kamfanin ya yi a Najeriya rayuwar ’yan kasar da dama ta inganta ta fuskar lafiya da tattalin arziki.

Ya ce kamfanin zai ci gaba da samar da ingantattun magunguna don tabbatar da ganin ’yan Najeriya sun samu lafiya da bunkasar arziki.

Da yake jawabi, daya daga cikin dillalan kamfanin mai kula da shiyyar Arewa da ya samu kyautar mota kirar jip, Muhammad Garba ya bayyana cewa jajircewa da kuma mayar da hankalin da ya yi wajen wayar da kan jama’a kan magungunan kamfanin ne suka janyo ya lashe kyautar motar.

Ya bayyana cewa ya yi rajista da Naira dubu hudu kacal, kuma cikin ’yan watanni ya zama babban dillalin kamfanin.

Ya ce alfanu da nasarorin da ya samu ta hanyar kamfanin suna da yawa, inda suka hada da samun bunkasar arziki da lafiya.

Ita ma da take magana jim kadan bayan ta karbi mukullin sabuwar motar da kamfanin ya ba ta, Princess Ebelyn Is Ehebha, ta bayyana cewa ta samu nasarar samun kyautar motar ne saboda kwazon da ta nuna wajen shigar da magungunan kamfanin.

Hakazalika, babban dillali, Mista Ajisefini Opeyemi ya bayyana cewa ya samu kyautar motarsa kirar Toyota ne saboda rawar da ya taka wajen shigar da kayan kamfanin, musammam ma a Kudu masu Yammacin kasar nan.Kamfanin ya raba kyaututtukan talabijin da lema da huluna da riguna da kuma wayar salula ga wadanda suka ci gasar reful da aka gudanar a wurin bikin.