Kamfanin bolkswagen zai dawo Najeriya

Bayan shekara fiye da 20 da barin Najeriya kamfanin kera mota na bolkswagen na kasar Jamus yana yunkurin dawo wa Najeriya don ci gaba da harkokinsa.Matakin ya biyo bayan sanya hannu a kan wata yarjejeniya da kamfanin ya yi da kamfanin Stallion Group don kafa masana’antar hada mota a shekara mai zuwa.Rugujewar yarjejeniyar ta farko […]

Kamfanin bolkswagen zai dawo Najeriya
Kamfanin bolkswagen zai dawo Najeriya

Bayan shekara fiye da 20 da barin Najeriya kamfanin kera mota na bolkswagen na kasar Jamus yana yunkurin dawo wa Najeriya don ci gaba da harkokinsa.
Matakin ya biyo bayan sanya hannu a kan wata yarjejeniya da kamfanin ya yi da kamfanin Stallion Group don kafa masana’antar hada mota a shekara mai zuwa.
Rugujewar yarjejeniyar ta farko tsakanin kamfanin bolkswagen da gwamnatin Najeriya ita ta janyo ya rufe masana’antarsa da ke Jihar Legas, daga bisani ya sayar da hannun jarinsa ga kamfanin Stallion Group.
A wata sanarwar da Kamfanin Stallion ya fitar a karshen makon jiya ya ce hadin gwiwa tsakananin kamfanonin biyu zai janyo a kafa masana’antar hada motocin kamfanin bolkswagen a Najeriya.
Sanarwa ta ce an samu ci gaban ne saboda sabuwar dokar sarrafa motoci da gwamnatin tarayya ta samar don ta karkafa gwiwar kamfanonin da suke son yin masana’antar motoci.
Sanarwar ta ce kamfanin bolkswagen ya kasance jagora a harkar kera motoci a nahiyar Turai da duniya baki daya.
Shugaban kamfanin Stallion, Mista Sunil baswani ya ce, “wannan wani abin farin ciki a wurin kamfanin Stallion, kasancewar ya yi hadin gwiwa da babban kamfanin kera motoci na duniya kamar kamfanin bolkswagen.”
Ya ce kamfanin Stallion a shirye yake ya cimma burin da ake so a Najeriya tare da fadada kamfanin wajen yin kere-kere a kasar.
Shugaban ya jaddada kudurinsa na yin aiki tare da gwamnatin Najeriya don samar da ayyukan yi da janyo masu sanya hannun jari don a bunkasa tattalin arzikin kasa.
Babban Daraktan ciniki na kamfanin a nahiyar Afirka na kamfanin bolkswagen, Dokta Jan Utermarck ya ce kamfanin ya dade yana binciken inda zai gudanar da kasuwancinsa, daga bisani sai ya gano cewa kamfanin Stallion shi ne kamfanin da zai hada gwiwa da shi a nahiyar Afirka da za a kafa masana’antar hada motoci a Jihar Legas daga shekara mai zuwa.
Kamfanin Stallion ya ce zai rika hada samfurin motocin Jetta da bolkswagen CC da Amarok a rukuni na farko, sannan a rukuni na biyu ya yi motocin Passat da Tiguan.