Kamfanin Chi ya gabatar da sabuwar madarar  Hollandia  mai saukin narkewa

Kamfanin Chi Limited yana ci gaba da kawo sababbin sauye-sauye inda ya kaddamar da sabuwar madarar Hollandia don iyali wacce ba ta dauke da sinadarin ‘Lactose’  kuma tana da saukin narkewa.  Wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce madarar ita ce irinta ta farko a Najeriya. Sanarwar ta ce bincike ya tabbatar da cewa […]

Kamfanin Chi ya gabatar da sabuwar madarar  Hollandia  mai saukin narkewa
Kamfanin Chi ya gabatar da sabuwar madarar  Hollandia  mai saukin narkewa

Kamfanin Chi Limited yana ci gaba da kawo sababbin sauye-sauye inda ya kaddamar da sabuwar madarar Hollandia don iyali wacce ba ta dauke da sinadarin ‘Lactose’  kuma tana da saukin narkewa.  Wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce madarar ita ce irinta ta farko a Najeriya.

Sanarwar ta ce bincike ya tabbatar da cewa ’yan Najeriya ba su saba amfani da sinadarin lactose ba don haka mafi yawa sindarin lactose na cikin madara ba ya narkewa. Wannan ya sa idan wadansu suka yi amfani da  sinadarin suke yawan gyatsa ko gudawa da sauransu. Kamfanin Chi ya ce mafiya yawan masu amfani da sinadarin ba su fahimci me yake jawo musu wadannan alamu ba saboda karancin fadakarwa. Wadanda kuma suke da masaniya a kan sinadarin sai ka ga sun daina amfani da madara da sauran sindarai da suke da dangantaka da wannan sinadari.

Sanarwar ta ce sakamakkon himma da Kamfanin Chi Limited ya yi wajen kawo wa abokan huldarsa madarar da dangoginta, an kaddamar da Hollandia wacce ba ta dauke da sinadarin lactose. Domin samar wa abokan hulda madarar da ta dace da su maimakon daina amfani da ita.

Daraktan Kamfanin Chi Limited Mista Deepanja Roy, ya ce sabuwar madarar Hollandia da ba ta dauke da sinadarin lactose mai saukin narkewa a Najeriya yana nuna  ’yan Najeriya za su sha madara mai dauke da sinadaran kula da  lafiya.

“Muna farin cikin sanar da kowa cewa a yanzu za a samu damar amfana da dukkan sinadarai masu gina jiki da suke cikin madarar. Hollandia da ba ta dauke da sinadarin ‘Lactose’ tana dauke da sinadarin da yake sa madara saurin narkewa, saboda tana dauke da  zallar madara da ba ta dauke da sinadarin lactose,”  inji shi.