Kamfanin Credit Direct A Matsayin Kasuwancin Zamani – Fasali Da Jami’ai
Alaka tsakanin mutum da mutum, ita ce zuciya da ruhin kasuwanci. Kai-tsaye, kasuwanci na gudana ne lokacin da daidaikun mutane ko rukunin mutane bisa radin kansu suke iya samar da hanyoyin da za su saukaka rayuwar wani mutum ta ya samu riba. Kasuwanci yana kawar da matsaloli da magance abubuwa masu kawo kunci da samar […]
Alaka tsakanin mutum da mutum, ita ce zuciya da ruhin kasuwanci. Kai-tsaye, kasuwanci na gudana ne lokacin da daidaikun mutane ko rukunin mutane bisa radin kansu suke iya samar da hanyoyin da za su saukaka rayuwar wani mutum ta ya samu riba. Kasuwanci yana kawar da matsaloli da magance abubuwa masu kawo kunci da samar kyakkyawar mu’amala da abokan ciniki, da samar da jin dadi ga abokin cinikin da aka hadu. Riba kan zo ne kawai lokacin da ingantaccen kasuwanci na zamani ya dace da jin dadin abokin ciniki. A Kamfanin Credit Direct Limited, ilimin abin da hakikanin kasuwanci yake nufi, shi yake sa muke kara gaba koyaushe, yake karfafa mu mu rika jijjifi da safe, mu zauna a hanya mu yi hakuri da manufa mai sauki ta zuwa ofis da sassafe gwargwadon iko don yi wa dimbin abokan cinikinmu hidima. Burinmu na yin aiki shi ne abin da zai karfafa ayarin masu sayar da kaya ba tare da damuwa da zafin rana a jihohin Sakwato, Gombe da Katsina ba, kuma mu kutsa zuwa yankuna masu ruwa na jihohin Bayelsa da Ribas don zakulo karin ’yan Najeriya don magance musu matsalolinsu na harkokin kudi. Farin ciki da annashuwa a fuskokin abokan ciniki lokacin da suka samu sanarwar ba su rancen da suka nema cikin ’yan awanni, su ne suka karfafa mahukuntanmu su rika aiki dare da rana suna bullo da sababbin hanyoyi don tabbatar da ksawanci ya cimma nasara tare da samar da cikakken jin dadi ga abokan ciniki. Duk da cewa ayarin ma’aikatan Kamfanin Credit Direct ka iya haduwa da cinkoson ababen hawa da zai rike su na awanni a Leags, tafiya zuwa sassan kasar nan don ziyartar masu ruwa-da-tsaki ko sanya kansu a hanya kunci don bin hanya har zuwa Arewa don ganawa da wani abokin kasuwanci da ke neman taimako, aikinmu ne na yin hidima da kula da abokan kasuwancinmu da tabbatar da cikar burin kowa da ke hulda da mu.
Manufar tsarin Kamfanin Credit Direct, ita ce cimma bukatun wadanda ba a kula da su da kuma wadanda suke da bukata ta hakika ta kudi amma ba za su iya samu ba, ba domin wani laifi nasu ba, sai don muguwar watsi da aka yi da su, da gibin da ke tsakanin wadatarwa da dimbin kasuwann da aka shirya da gangan don a tabbatar da cewa a koyaushe akwai ’ya’yan bora a cikin jama’a yayin aiwatar da manufofin kasa.
Kamfanin Credit Direct zai ci gaba da cike gibin tare da yin abin da abin da jama’a ciki har da kwararru suke ganin “BA MAI YIWUWA” ba ne a cimma haka da abin da tsofaffin masu masana’antu suke ganin cikakkiyar asara ce idan aka yi shi. Bilhasali ma lokacin da muka faro, tsawo wata shida, abin da muka tsara ya kasance a hannun manyan shugabannin ’yan kasuwa da manyan jami’an gwamnati, kuma hukuncin da suka yanke shi ne “in kuka yi haka ku kuka jiyo,” me ya jawo wannan tsoro, kuma yaya aka yi muka canja wannan tunani? Amsar mai sauki ce, saboda batun shi ne ba don ‘riba’ ko ‘asara’ ba ce, ba don ribar da za a samu a karshen shekara ba ce, ba an kafa shirin ne don taron almubazzaranci na Hukumar Gudanar na Shekara-Shekara ba, an tsara shi ne don sanya farin ciki a zukatan ma’aikata masu daukar albashi wadanda su ne hakikanin masu juya tattalin arziki a Najeriya. A kawo natsuwa da cikar buri ga wanda dansa yake kwance a gadon jinya kuma ba zai iya samun kular likita sai ya ba da kudin ajiya. Da kuma mahaifiyar da ke wajen aiki kullum kuma ba za ta iya biyan kudin makarantar danta ba da ke zuwa makaranta daga ranar farko na karshen shekaran karatu inda za a hana shi rubuta jarrabawa kawai saboda ba a biya albashi ba. Da wanda yake kokari wajen aikin gwamnati kuma lokacin biyan kudin haya ya yi, mai kula da gidan ya ba shi lokaci kankane.
Wadannan su ne suka cancanci taimako, kuma mun yi babban rajista ta sunayen fittatu a jihohi daban-daban wanda ba su san yadda za su yi ba har sai sun samu rance a wannan rana ko lokaci.
Ba zan taba mantawa da wani cikin abokan kasuwancinmu ba da ya zo wani ofishmu na Arewacin kasar nan yana kuka cewa dansa guda daya da yake da shi yana gadon asibiti kuma har sai ya biya kudi za a yi masa aiki idan ba a biya ba zai rasa ransa, yana ta lallashi da roko a ba shi rance, muka zaunar da shi a natse muka ba shi fom ya cika muka bukaci wasu takardu don haka ya yi sauri ya dauko. Cikin awa biyu ya dawo bayan cika fom, ya zauna yana sauraren abin da zai biyo baya, ya zagaya cikin bankin yana yin addu’a wajen misalin karfe 3:45 a ranar ya samu kudin ya tashi da murna yana jin dadi, ya kai gwiwa kasa yana godiya da jin dadi to wannan shi ne burinmu, wannan shi ne nasarar da muka samu a wannan rana.
Kamfanin Credit Direct ya fi yadda ya kamata ba tare da wata matsala ba muka ba mutanen da ke da bukatar rance na tsawon shekara hudu (daga Afrilun 2007 zuwa Disamban 2011) kuma mu ne muka zama na farko a cikin kamfanonin da suke harkar ba da rance, wannan shi ne shaida na kamfanin da ya sa biyan bukatun abokan kasuwancinsa a gaba kafin samun riba a cikin harkar kasuwanci, shi ne abu na farko hanya guda daya. samun nasaranmu ya sa wasu suke binmu a baya, kuma ya sa muke gasa da masu ba ’yan kasuwa rance, muna sun yin gasa, domin mu, ba muna so ya zama mu kadai ba ne a fagen sai don magance matsololin tattalin arziki. Don haka, wadansu suke so su shiga gabanmu, mun kara fadada wa abokan kasuwancinmu da kula da su da kara kusantarsu. Mun shirya taron masu hannu jari a ciki don bunkasa yanayi, domin kara fahimtar abokan kasuwanci da kara jarinmu. Mun bunkasa makarantu da ba su kayan aikin da suke bukata na dalibai, da ba da damar duba lafiya kyauta ga abokan hulda, mun ba su horo na musanman (malamai da kwararru) kan hanyar samar da sarrafa abubuwa daban-daban, mun ba dalibai damar zuwa karatu kyauta domin na bayansu su dage da karatu da haka za su gane akwai sakamako kan duk abin da ka dage. Mun ba da littafain karatu da ba da dama ga masu matsaloli bakin kokarinmu. Mun dauki nauyin abubuwa daban-daban da aikace-aikace ga wadanda suka cancanci mu taimaka mawa. Yin hakan don mu sa wa abokan hulda farin ciki kuma muna so duk bayan shekara ya fi haka.
Mun tsaya wajen ganin biyan bukatar abokan huldarmu da ma’aikatanmu “babban jarinmu” suka tsaya wajen ganin cimma burinmu da gina kasa daga Arewa zuwa Kudu da Yammacin kasar nan, daga abin da ya raba mutum da kasar Nijar da Delta zuwa Arewa, lallai, muna da jajirtattun ma’aikata wadanda suka sadaukar da kansu wajen ci gaban abokan hulda da sayar da kayan kamfani gaba daya.
Kamfanin Credit Direct bai ba mu matsala ba kuma ya samu karbuwa wa fiye da sauran kamfanoni irin namu
Hanyar yin kasuwancinmu da ya bambanta shi ya sa muka samu abokan kasuwanci kamar miliyan a kasar nan wadanda su ne karfin Kamfanin Credit Direct na ’yan uwa. Mun kirkiri hanyoyin da za mu karfafa rance don ba ma abokan hulda natsuwa.
Abokan kasuwancinmu su ne nasarar ci gabanmu. Muna samun karfin gwiwa daga gare su.
Mu ne Kamfanin Credit Direct Limited, kamfanin na daya a Najeriya wajen bayar da rance ga mabukata.