Kamfanin da ya daina aiki aka ba kwangilar titin Abuja-Kaduna

Kamfanin da ya samu aikin aikin na Naira biliyan 252.89, ƙarfin jarinsa Naira dubu ɗari ne kacal, kuma ya kai matakin a soke lasisinsa a hukumance.

Kamfanin da ya daina aiki aka ba kwangilar titin Abuja-Kaduna

Binciken da wakilanmu suka gudanar ya nuna sabon kamfanin da Gwamnatin Tarayya ta ba wa kwangilar gyara titin Abuja zuwa Kaduna a kan Naira biliyan 252.89, ya jima da daina aiki.

Binciken ya gano kamfanin da ya samu aikin aikin na Naira biliyan 252.89, ƙarfin jarinsa Naira dubu ɗari ne kacal, kuma ya kai matakin da Hukumar Kula Rajistar Kamfanoni (CAC) zai soke lasisinsa a hukumance.

A kwanakin baya ne Gwamantin Tarayya ta ƙwace aikin daga Kamfanin Julius Berger saboda rashin daidaitawa kan farashi, inda ta ba wa Infoquest Nigeria Limited.

Ministan Ayyuka, David Umahi ya sanar cewa Infoquest ne kamfanin da ya yi nasarar samun aikin daga cikin kamfanonin da suka nema.

An ba da aikin kammala titin Abuja zuwa Kaduna ne a matsayin rukuni na biyu na aikin gyaran babban titin Abuja-Kaduna-Zariya-Kano, wanda da farko aka ba wa Julius Berger tun a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Sai dai a wata sanarwa da kamfanin Julius Berger ya wallafa a manyan jaridun Najeriya, ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki da faɗuwar darajar Naira sun haifar da tashin farashin makamashi da kayan aiki.

Sanarwar ta kara da cewa duk da alƙawarin da Gwamnatin Tarayya ta yi na ba kamfanin Naira biliyan 20 a duk wata domin kammala aikin cikin watanni 14, gwamnatin ba ta bashi ko sisi ba tun daga watan Nuwambar 2023.

A makon jiya ne Ministan Ayyuka David Umahi ya bayyana cewa Kamfanin Infoquest Nigeria Limited ya yi nasarar samun aikin a kan Naira biliyan 252.89, bayan an ƙwace daga hannun Julius Berger.

Umahi wanda ya sanar da haka yayin rangadin titin ya ce Hukumar Kula da Kwangilar Gwamnatin Tarayya (BPP) ta ba wa Infoquest takardar shaidar ‘amincewa’, wanda za a gabatar a zaman Majalisar Zartaswa ta Kasa da ke tafe domin sahalewa.

Dokar Kwangilar Gwamnati ta 2007 ta fassara ma’anar ‘Amincewa’ a matsayin an cika ka’idodin dokar wajen neman aiki, kuma Hukumar BPP ta amince a bayar da shi. Wannan na nufin amincewar Hukumar a ba wa kamfanin aikin ya fara kuma a biya shi kuɗin aikin.

Matsayin Kamfanin Infoquest

Amma binciken da wakilanmu suka gudanar a Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni ta Ƙasa (CAC) ya nuna kamfanin ya faɗa cikin kamfanoni marasa aiki, a shafin CAC. Hakan na nufin ba wa kamfanin aikin ya saɓa Dokar Kamfanoni ta Kasa (CAMA) ta Shekarar 2020.

Binciken ya kuma gano cewa hannun jari guda 100,000 da darajarsu ta kai Naira dubu ɗari kacal ne a kamfanin Infoquest. Shafin CAC ya kuma nuna cewa tun da aka kafa kamfanin bai taɓa biyan kuɗin ka’ida na shekara shekara ba ga hukumar.

Me doka ta ce?

Dokar CAMA 2020 ta bayyana cewa duk kamfanin da ba ya aiki, ba shi da ƙarfin gudanar da wani sabon aikin kwangila ko kasuwanci a ƙarƙashin doka,

Don haka ba wa Infoquest Nigeria Limited aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna ya ci karo da Sashe na 525(3) & (4) na dokar CAMA 2020, wadda ta ba wa Hukumar CAC ikon soke kamfanonin da ke wannan matsayi daga rajistarta. Da zarar CAC ta soke kamfani daga rajistanta, to babu shi, ya zama tarihi kuma ba zai iya karɓar aiki ko aiwatar da aiki ba.

Sashe na 526 kuma ya bayyana cewa idan aka soke rajistar kmafani daga rajistan CAC, to kadarorinsa sun koma mallakin Gwamanti.

Sashe na 583 kuma ya bayyana cewa duk kamfanin da ya gaza cika shatuɗan da doka da gindaya ta ba shi da ’yancin aiwatar da kwangila ko kasuwanci. Hanyar kawai da kamfanin da aka soke zai iya gudanar da aiki, shi ne idan ya samu umarnin kotu da ya sake dawo da shi cikin rajista, ka at yadda Sashe na 583(a) na dokar ya bayyana.

Matsayin kamfanin Infoquest

A makon da ya gabata ne Umahi ya sanar cewa Kamfanin Infoquest Nigeria Limited ne ya yi nasara a cikin kamfanoni shida da suka nemi aikin gyayan titin. Kamfanonin a cewarsa su ne: Julius Berger Nig. Plc, Hitech Construction Company Limited, Infoquest Nigeria Limited, CBC Nigeria Limited, CCECC Nigeria Limited da kuma CGC Nigeria Limited.

Binciken da muka gudanar ya nuna a shekarar 1997 aka yi wa kamfanin rajista da lambar RC 315362. Sai dai kuma shafin Hukumar CAC ya nuna kamfanin ba ya aiki. Adireshin kamfanin da ke shafin na CAC shi ne gida mai lamba 39, Layin Falohun, Orile, Legas.

Kamfanin na da daraktoci uku: Omeruwa Onyekachi, Olubodun Benson, da kuma Kuforiji Moses.

Sai dai kuma babu bayanan kamfanin a intanet, wanda hakan ya sanya alamar tambaya game da halascinsa da karfinsa wajen gudanar da aikin na biliyoyin Naira. Su kansu daraktocin babu bayansu da suka taka kara suka karya a kafofin intanet.

 

Wakilanmu: Sagir Kano Saleh, Faruk Shuaibu, Musa Luka Musa, Abbas Jimoh, Balarabe Alkasim (Abuja), Dotun Omisakin (Legas)