Kamfanin Daily Trust da Ma’aikatar Gona ta Kebbi sun yi bikin nunin amfanin gona
Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yaba wa Kamfanin buga Jaridun Daily Trust da kuma Ma’aikatar Kula da Harkokin Noma ta Jihar Kebbi, wajen hada hannu domin ba da gudummuwarsu ga manoman jihar. Gwamnan ya yi wannan yabo ne a yayin wani taro da Kamfanin Daily Trust tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Kula […]
Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yaba wa Kamfanin buga Jaridun Daily Trust da kuma Ma’aikatar Kula da Harkokin Noma ta Jihar Kebbi, wajen hada hannu domin ba da gudummuwarsu ga manoman jihar.
Gwamnan ya yi wannan yabo ne a yayin wani taro da Kamfanin Daily Trust tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Kula da Harkokin Noma ta Jihar Kebbi suka shirya domin amfanin manoman Jihar ta Kebbi.
Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya ce, kamfanin Daily Trust da Aminiya ya ba da gagarumar gudummawa a kasar nan wajen wayar da kan manoma ta fannin aikin gona, kamfanin ya kuma kara fito da Jihar Kebbi a idon duniya a kan harkokin noma, ya kuma ce babbar gudummuwar da kafafen yada labarai suka ba da yana daya daga cikin nasarorin da Jihar Kebbi ta samu a fannin noma.
Gwamnan ya ci gaba da cewa idan da ba a samu ire-iren Kamfanin J Daily Trust ya ba su goyon ba to da zai yi matukar wahala mutane su san irin kokarin da manoman Jihar Kebbi yi.
Gwamnana ya ce, saboda yayatawar da kafofin yada labarai suka yi ta yi a kan wannan shiri na noman rani, yana daya daga cikin ci gaban da harkar noma ya samu a Jihar Kebbi, shi ne hadin gwiwar tsakanin Jihar Kebbi da ta Lagos don yin shiri na musamman kan hada kai domin kulla huldar kasuwanci kan amfanin gona, inda kuma daga bisani jihohin biyu suka amince da yin kawancen noman shinkafar don cimma nasarar da ake bukata.
Wannan yarjejeniyar wata fitilace aka haska ga sauran jihohin Najeriya wajen kasuwanci kan amfanin gona da ake nomawa a cikin kasar nan tare kuma da samar da ayyukan yi ga marasa aikin yi, a kuma rage zaman kashe wando ga daruruwan matasan kasar nan.
Har ila yau Gwamnan ya ce, wannan kawance wata hanya ce aka fito da ita don kara wa kasuwanci kwarin gwiwa da kuma kara samar da hanyoyin walwala da jin dadin al’ummar jihohin biyu da kuma farfado da arzikin kasa ta hanyar noma abincin da zai wadatar da mutanen kasar nan baki daya.
Ya ce, wannan hadin gwiwa tsakanin Jihar Kebbi da Jihar Lagos ta samar da shinkafa a babban kasuwar nan ta Lagas da ake cewa Lake Rice. Haka zalika shirin noma a Jihar Kebbi sai kara samun nasarori yake yi, ta inda ake samun masu saka hannun jari ga harkar noma domin bada tasu gudummawa irin su kamfanin Labana Rice Mills da kuma kamfanin Wacot Rice da kuma wanda Dangote ke ginawa yanzu a garin Dugu Raha da wanda ake yi a garin Kamba. Duk wadannan kamfanoni sun shigo Jihar Kebbi ne domin yadda kafofin yada labarai ke yayata aikin noma na Jihar Kebbi. A karshe gwamnan ya ce, noma da ma’adanai su ke kan gaba cikin abin da Gwamnatin Jihar Kebbi ke bai wa muhimmanci.
Da yake nasa jawabin, Shugaban Kamfanin Daily Trust, Alhaji Mannir Dan’Ali, ya ce wannan taro na manoma ne, saboda haka yana kara jan hankalin manoman Jihar Kebbi da su kara bada goyon baya dari bisa dari ga kokarin da Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kebbi ke yi wajen aikin noma, ina tabbatar maku da cewar kafofin yada labarai irinmu, zamu ci gaba da kokari domin tallafa maku wajen sanar da duniya irin namijin kokarin da kuke yi a kullum akan harkar noma. “Na kuma ji dadi yadda manya-manyan manoman Kebbi irin su Alhaji Abdul Yan’Besse da Alhaji Sani Aliyu da sarkin Wasagu da Hajiya Kulu Wasagu da dai sauran manoma suka sami damar halartar wannan taro.
A cikin nasa jawabinsa, Ministan aikin gona Cif Audu Ogbeh wanda babban Darakta na ma’aikatar aikin gona ta tarayya, Injiniya Abdullahi Shehu ya wakilta, ya ce wannan taro da ma’aikatar aikin gona ta Jihar Kebbi da kuma Kamfanin Daily Trust suka shirya, yana da muhimmanci kwarai da gaske ga manoma, domin za su karu ainun ta inda za su sami cigaba akan aikin noma da kuma hanyoyin da gwamnati za ta kara taimaka masu.
Ministan ya ce a shekarar da ta gabata, Jihar Kebbi an ware mata Naira Biliyan 4 na kudin taki domin a bai wa manoman jihar kawai, amma daga karshe takin da aka samu na Naira Miliyan 500 ne kawai suka samu, wannan ya faru ne saboda yawancin manoman ba su da waya kuma Gwamnati ta ce sai kana da waya kana za a baka taki, domin ta waya ne za a aiko maka da sako ta inda zaka je ka karbi takin.
Ministan ya ci gaba da cewa, “saboda rashin waya Biliyan 3 da rabi ya tafi a banza, saboda haka manoma idan kuna son ku ci gajiyar bayar da takin zamani, to ku sayi wayoyin hannu idan baka da waya baka da taki.”
A karshe ministan ya ce karfin manomi a wurin noma shi ne takin zamani, idan manomi ba shi da taki to ba shi da noma ingantacce, kuma ku kananan manoma da ku ne gwamnati ke takama da ku, domin ku ke ciyar da kasar nan, kayan amfanin gonar ku ne jama’a ke saye suna ci, amma manyan manoma kamfanoni ke sayen amfanin gonar su.
Wani manomi mai suna Abubakar Besse wanda wakilinmu ya zanta da shi a wurin taron, ya ce tun da yake zuwa wurin taron manoma bai taba samun wayar da kai ba irin na wannan taro da Kamfanin Jaridar Daily Trust da Ma’aikatanr Aikin Gona suka shirya, yana mai cewa ya gamsu da irin jawaban da manyan baki suka yi masu, ya kuma yabawa kamfanin Jaridar Daily Trust da Ma’aikatar Aikin Gona ta Jihar Kebbi, domin sun yi rawar gani sosai wajen kara wayar da kan manoman jihar Kebbi da kuma tallafin da Gwamnatin tarayya da jiha ke ba su tun daga wurin noman shinkafa har zuwa sayar da ita.