Ba samame EFCC ta kai ofishinmu ba —Kamfanin Dangote

Rukunin Kamfanonin Dangote ya bara kan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zuwan jami’an EFCC ofishinsa kan binciken badakalar canjin kudi a zamanin Emefiele

Ba samame EFCC ta kai ofishinmu ba —Kamfanin Dangote

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote

Rukunin Kamfanin Dangote ya ce a shirye yake ya taimaka wa Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) a binciken da take yi kan badakalar canjin kudi.

Kamfanin Dangote ya sanar da haka ne bayan ce-ce-ku-cen ya biyo bayan ziyarar da jami’an EFCC suka kai a babban ofishinsa da ke Legas a ranar 4 ga watan Janairu.

Jami’an EFCC sun je babban ofishin kamfanin ne a wani bangare na binciken da hukumar ke yi kan wasu kamfanoni 52 game da canjin Dala da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba su a zamanin tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele, shekaru 10 da suka gabata.

Wata sanarwa da Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na kamfanin Anthony Chiejina, ya fitar a ranar Lahadi ta ce neman magana ne ya kai jami’an EFCC ofishin kamfanin a daidai lokacin da wakilansa suka riga suka kai wa hukumar takardun da take nema.

Don haka ta bukaci masu ruwa da tsaki su kwantar da hankalinsu, su yi hakuri, gami da alkawarin sanar da su duk halin da ake ciki.

Sanarwar ta ce a ranar 6 ga watan Disamba, 2023 kamfanin ya samu takardar EFCC na neman cikakken bayanin duk canjin Dala da CBN ya ba kamfanin daga 2014 zuwa lokacin.

A cewar sanarwar, hukumar ta kuma aike wa sauran kamfanoni 51 da abin abin ya shafa irin wannan takardar.

Kamfanin a cewarsa, ya amsa bukatar ta EFCC amma ya nemi karin haske kan rassansa ko sassansa da ake bukatar bayanai a kansu da kuma karin lokaci don hadawa da kuma gabatar da bayanan na shekaru 10, kasancewar an nemi bayanan ne a kurarren lokaci.

“Amma EFCC ba ta amsa bukatarmu ta karin wa’adin ba, inda ta ce dole mu ba da bayanan a lokacin da ta kayyade.

“Duk da haka muka ba ta tabbacin ba da bayanan a rukuni-rukuni a yayin da muke fadi-tashin kammala hada su.

“Ranar 4 ga wata jami’anmu suka kai wa EFCC kashin farko na takardum, amma jami’an hukumar suka ki karba, suka ce dole ofisoshinmu za su zo su karba kai-tsaye.

“Wakilan namu suna can jami’an hukumar suka zo ofishinmu neman takardun a wanda hakan tozarci ne na babu gaira, babu dalili.”

Kamfanin ya jaddada cewa, a saninsa, ba a tuhumi wani kamfani ko sashe da ke karkashinsa da aikata ba daidai ba, kuma a matsayinsa na mai bin doka da oda, zai ci gaba da bai wa EFCC hadin kai da dukkan bayanan da suka dace.

“Mun riga mun kai kashin farko na takardun kuma muna aiki tukuru don hadawa da mika sauran a kan lokaci, domin taimaka wa binciken nasu.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja