…Kamfanin dangote ya yi alwashin bunkasa noma a Najeriya
Kamfanin dangote ya yi alwashin bunkasa noma a Najeriya bayan kamfanin ya kaddamar da shirinsa na inganta noma a kasar nan. Kamfanin ya ce nan gaba kadan Najeriya za ta dogara da kanta ba tare da shigo da abinci daga kasashen waje ba.Kamfanin ya kuma jaddada kudurinsa na taimaka wa shirin gwamnatin taryya na bunkasa […]
Kamfanin dangote ya yi alwashin bunkasa noma a Najeriya bayan kamfanin ya kaddamar da shirinsa na inganta noma a kasar nan.
Kamfanin ya ce nan gaba kadan Najeriya za ta dogara da kanta ba tare da shigo da abinci daga kasashen waje ba.
Kamfanin ya kuma jaddada kudurinsa na taimaka wa shirin gwamnatin taryya na bunkasa noma a kasar nan.
A yanzu kamfani ya zuba jari wajen samar da takin zamani da noman shinkafa da sarrafa tumatir da samar da siga da sauransu.
Kamfanin yana kan gina matatar mai da za ta samar da gangar danyen mai dubu 650 a rana, wadda za ta zama mafi girma a duniya.
A bara ne kamfani ya cimma wata yarjejeniya da Ma’aikatar Gona da Bunkasa Karkara ta tarayya, inda ya zuba jarin Dala biliyan 1 wajen noman shinkafa da sarrafa ta a kasar nan.
Wata sanarwa da kamfanin ya fitar ya bayyana cewa ya sayi gonaki a Jihar Edo da Jigawa da Kebbi da Kwara da kuma Neja, inda fadin gonakan ya kai hekta dubu 150 don bunkasa noma a kasar nan.
Kamfanin ya yi alkawarin samar da injinan da za su rika sarrafa shinkafa mai yawan metric-tan 120 a kowace rana, tare da rubanya adadin cikin shekara biyu.