Kamfanin Eagleserbe Consultants ya samu lasisi
Wani kamfanin harkokin kasuwanci da sadarwa na Arewa mai suna Eagleserbe Consultants Limited ya samu lasisin amincewa daga kungiyar Kamfanonin Tallace-Tallace ta Najeriya (AAAN) domin ya gudanar da harkokin tallace-tallace da kasuwancin harkokin sadarwa a kasar nan. Manajan Daraktan kamfanin wanda ya kware wajen bincike da harkokin kasuwanci, Yarima Shola Rotimi, wanda ya shaida […]
Wani kamfanin harkokin kasuwanci da sadarwa na Arewa mai suna Eagleserbe Consultants Limited ya samu lasisin amincewa daga kungiyar Kamfanonin Tallace-Tallace ta Najeriya (AAAN) domin ya gudanar da harkokin tallace-tallace da kasuwancin harkokin sadarwa a kasar nan.
Manajan Daraktan kamfanin wanda ya kware wajen bincike da harkokin kasuwanci, Yarima Shola Rotimi, wanda ya shaida wa wakilinmu haka, ya ce kamfanin zai taka rawa sosai wajen ingantawa da samar da sakamako mai kyau da riba mai yawa ga abokan huldarsa.
Kasancewarsa cibiyar bincike, kamfanin yana aiki da cikakkiyar lura da bukatun abokan hulda da halayyarsu, kuma hakan zai saukaka masa wajen ingantawa da kawo canji mai ma’ana.
Ya ce, “Muna farin cikin sanar da masu harkar tallace-tallace da harkokin sadarwa cewa sakamakon samun lasisi da amincewa don zama mamba a Cibiyar Kamfanonin Tallace-Tallace ta Najeriya (AAAN), hakan ya samu ne sakamakon rawar da muke takawa wajen samar da ingantaccen aiki da sakamako mai kyau da samar da babbar riba da kuma kokarinmu da gogewarmu ta sanin buri da halayyar dimbin abokan huldarmu.”
Yarima Rotimi ya bayyana cewa kamfanin Eagleserbe Consultants Limited, a matsayinsa na kamfanin da ya kware a harkokin kasuwanci da sadarwa ta Intanet ya shahara wajen ganowa da gyarawa da bayar da shawarwarin da za su yi dalla-dallar adadi a alluna. “Adadi ba su karya, don haka muke samar da sakamako mai yawa, kuma muna kokarin gina lafiyayyiyar kasuwa mai kawo riba mai gwabi,’ inji shi.
Game da yadda kamfanin Eagleserbe Consultant ya yi fice wajen gudanar da ayyukansa na talla (USO), Yarima Rotimi ya ce, “Hangen nesanmu ne ya jawo mana yin fice, kuma mu wata cibiya ce ta bincike da ke amfani da dabaru daban-daban da ya dace da kowane irin kaya da ake son tallatawa.”
Yarima Rotimi ya ce, “A matsayinmu na wata cibiyar bincike kuma cibiyar tsara tallace-tallace, kamfanin Eagleserbe Consultants yana tsarawa da bunkasawa ta hanyar zurfafa binciken bayanai domin zakulo sababbin dabaru da suke ba abokan hulda haske domin inganta taka rawa a fagen harkokin sadarwa. Muna da dabarun kirkira ta amfani da hanyoyinmu na nazari da bincike domin fito da kazar-kazar da gogewa ga wadanda ake son isa gare su. kwarewarmu da gogewar ma’aikatanmu da hanyoyin gudanar da bincike da dabarun kirkira da ake amfani da su wajen zakulo bayanai kan taken kamfe da jan hankali da sabar kafar labarai da wadanda ake isar da sako gare su, suna karfafa mu wajen yin tasiri a tsakanin jama’a da dominsu ake yi.”
Manajan Daraktan, Shola Rotimi wanda kwararre ne a fagen dabarun kasuwanci da sadarwa a tsakanin jama’a, ya yi digirinsa na farko ne a sashin kididdiga na Jami’ar Ilori, sannan ya yi digiri na biyu a harkokin kasuwanci tare da gudanar da bincike a kan kasuwanci. Kuma mamba ne Cibiyar Hulda da Jama’a ta Najeriya da kungiyar Masana kididdiga ta Najeriya, kuma cikakken mamba a Majalisar Masu Gudanar da Tallace-Tallace ta Najeriya.