Kamfanin Emirates ya dakatar da aiki a Najeriya kan rikicin kudi

Kamfanin sufurin jiragen sama na Emirates ya dakatar da harkokinsa a Najeriya saboda rike masa Dala miliyan 85 a kasar.

Kamfanin Emirates ya dakatar da aiki a Najeriya kan rikicin kudi

Kamfanin sufurin jiragen sama na Emirates ya dakatar da harkokinsa a Najeriya saboda rike masa Dala miliyan 85 a kasar.

Kamfanin ya ce zai dakatar da zirga-zirgar jiragensa a Najeriya daga ranar 1 ga Satumba, 2022 saboda Babban Bankin Najeriya ya ki sakar masa kudinsa daga Najeriya.

Idan dai za a iya tunawa, kamfanin a wata takarda da ya aike wa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, ya ce zai rage jigilarsa a Najeriya daga 11 zuwa bakwai zuwa tsakiyar watan Agusta, saboda Dala miliyan 85 dinsa da suka makale a kasar.

Akwai yiwuwar wasu kamfanonin jiragen na iya bin sawun Emirates saboda rike musu sama da Dala miliyan 600, da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kasa cika musu bukatarsu ta sauya kudaden zuwa Dala.

Bisa yarjejeniyar da aka kulla ta sufurin jiragen sama tsakanin kasashe (BASA), kamfanonin jiragen sama na kasashen waje za su sayar da tikitinsu a Naira yayin da CBN ke ba su kwatankwacin kudaden a Dala don kaiwa kasashensu.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a safiyar ranar Alhamis, Emirates ya ce zai sake yin nazari kan matakin da ya dauka idan har aka samu wani ci gaba mai kyau a cikin kwanaki masu zuwa.