Kamfanin Etisalat ya bayar da kyautuka ga kamfanonin da suka lashe gasar kirkira
Kamfanin wayar salula na Etisalat ya karfafa gwiwar wadanda suka yi nasarar lashe gasar kirkira ta Afirka ta shekarar 2014, inda ya ba su Dala dubu 35 don su inganta kirkirar da suka yi. Kamfanin Edammate da kamfanin Interactibe Media Interface Design su ne ya lashe gasar karo na uku yayin da aka yi bikin […]
Kamfanin wayar salula na Etisalat ya karfafa gwiwar wadanda suka yi nasarar lashe gasar kirkira ta Afirka ta shekarar 2014, inda ya ba su Dala dubu 35 don su inganta kirkirar da suka yi.
Kamfanin Edammate da kamfanin Interactibe Media Interface Design su ne ya lashe gasar karo na uku yayin da aka yi bikin mika kyautar a wata liyafar cin abinci da aka gudanar a kasar Afirka ta kKudu a makon da ya gabata.
Kamfanin Eitsalat ya kirkiro gasar ne don ya karfafa mutane wajen kirkira ta musamman a kasuwannin Afirka.
Kyautar farko da kamfanin ya bayar ta kunshi Dala dubu 25 ga wanda ya kirkiro wata haja ta musamman, inda kamfanin Edammate ya lashe yayin da ya kirkiro jadawalin jarabawar share fagen shiga jami’a.
Kyauta ta biyu ta kunshi Dala dubu 10 ga wanda ya kirkiro wata haja, inda kamfanin Interractibe Media Interface Design ya lashe ta yayin ya kirkiro wata karamar manhajar da ke samar da na’urorin biyan kudi ta yanar tauraron GPRS.
Manyan daraktocin kamfanin biyu Oluwale Rawa da Adia Sowho su ne suka mika kyautar a madadin kamfanin tare.
Darakta Oluwale Rawa ya bayyana farin cikinsa na ganin gasar ta karfafa gwiwar masu kirkira a fannonin daban-daban.
Ya ce kamfanin zai ci gaba da tallafa wa kamfanoni don kirkirar abubuwa da dama da za su taimaka wa jama’a.