Kamfanin Facebook ya nemi afuwar mutane kan katsewar ayyukansa
Kamfanin ya yi alkawarin gujewa faruwar irin haka a nan gaba.
Kamfanin Facebook, wanda ya mallaki shafukan sada zumunta na WhatsApp, Facebook da Instagram, ya nemi afuwar abokan huldarsa, bayan da kafafen suka daina aiki na tsawon wasu sa’o’i, a ranar Litinin.
Sanarwar da kamfanin ya fitar a cikin daren ranar Litinin, ya ce matsalar ta auku ne sakamakon wasu ’yan gyare-gyare da kamfanin ya yi.
- Yadda mai juna biyu ta shirya garkuwa da kanta a Yobe
- Mu ne ruwan jakara – a sha a birni, a sha a kauye
Sai dai wasu na zargin kamfanin na Facebook da rashin daukar matakan da suka dace, duk da masaniyar da yake da ita game da yada labaran karyar da ake yi a dandalinsa.
Kazalika, ana zargin dandalin da ba kananan yara damar cin karensu babu babbaka ba tare da daukar mataki ba.
Tun bayan katsewar shafukan na Facebook, WhatsApp da kuma Instagram, bayanai sun nuna yadda miliyoyin jama’a suka tsinci kansu cikin damuwa.
Mai magana da yawun kamfanin na Facebook, Andy Stone ne ya bada hakurin, inda ya ce kamfanin zai yi kokarin magance faruwar hakan a gaba.
Wannan shi ne karo na biyu da shafukan suke daina aiki a shekarar 2021, wanda ko a watan Maris sai da hakan ta faru na tsawon sa’o’i biyu.
Kazalika, mai Kamfanin, Mark Zuckerberg rahotanni sun ce ya tafka asarar Dala miliyan bakwai baya daina aikin shafukan.