Kamfanin Facebook zai kula da harshen Hausa

Sakamakon yadda harshen Hausa ke kara bunkasa a duniya da yadda ya zama daya daga cikin manyan harsunan Afirka 27 da ake mu’amala da su shafin Facebook, kamfanin ya fara shirye-shiryen inganta yadda ake mu’amala da harshen a kafar tasa. Kamfanin na Facebook ya ce yana shirin daukar ma’aikata sama da 100 domin mayar da […]

Kamfanin Facebook zai kula da harshen Hausa

Shugaban Qasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa da Shugaban Kamfanin Facebook Mark Zuckerbarg, a lokacin da ya zo Najeriya shekarun baya

Sakamakon yadda harshen Hausa ke kara bunkasa a duniya da yadda ya zama daya daga cikin manyan harsunan Afirka 27 da ake mu’amala da su shafin Facebook, kamfanin ya fara shirye-shiryen inganta yadda ake mu’amala da harshen a kafar tasa.

Kamfanin na Facebook ya ce yana shirin daukar ma’aikata sama da 100 domin mayar da hankali kan rubuce-rubucen da ake yi a shafin cikin harshen Hausa da wasu harsuna uku na Afirka.

Binciken gidan rediyon BBC ya tabbatar da ce mahukuntan kamfanin Facebook sun gaza wajen dakile labarun karya da na nuna kiyayya a kafar tasu, musamman ma dangane da harshen Hausa, don haka ne suke kokarin inganta tsarin, yadda za su samu nasara a nan gaba.

Binciken ya nuna cewa Facebook tare da hadin gwiwar wani kamfani da ke taya su tantance rubutu a harsunan Afirka, yana da mutane hudu ne kacal da ke bitar rubuce-rubucen da ake yi.

Ko a bara, kasashe da dama sun sanya dokokin da suka shafi shafukan sada zumunta ciki har da shafin Facebook a kasarsu.

Wani kwamiti na Majalisar Dattawan Amurka ya taba gayyatar shugaban kamfanin Facebook, Mark Zuckebarg, inda ya nemi ya amsa tambayoyi.

A farkon bana ne Facebook ya bayyana aiwatar da wasu sababbin tsare-stare domin magance katsalandan a zabubbuka a kasashen Najeriya da Ukraine da Indiya. Kamfanin ya bayyana cewa a kullum yana koyon abubuwa da dama daga jama’a kuma yana kokarin inganta kafar tasa.