Kamfanin gishiri na Dangote ya gwangwaje kwastomominsa
Kamfanin ya gwangwaje abokan hulɗarsa da kyaututtuka daban-daban.
Kamfanin gishiri na Dangote wato NASCON Allied Industries, ya baiwa abokan cinikinsa 50 kyautar Motoci da biliyoyin Naira, saboda jajircewarsu wajen sayar da kayayyakinsu daban-daban.
An gudanar da bikin karrama abokan ciniki na shekarar 2025 wanda fitaccen mai masana’antu kuma Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da mataimakin sthugabansa, Olakunle Alake suka halarta.
- HOTUNA: Har yanzu gobara na ci gaba da ci a Kasuwar Singa da ke Kano
- ‘’Yan banga sun buga min ƙusa a kai saboda kaza’
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Mista Aliko Dangote ya ce wannan rana ce ta kyautatawa abokan ciniki inda ya bayyana irin muhimmancin da kamfanin yake bayarwa wajen kyautatawa abokan cinikinsa.
Shugaban ya kuma yaba wa shugaban hukumar gudanarwa da ma’aikatansa saboda jajircewarsu, ƙwarewa, da kuma gudummawar da suka bayar ga ci gaban kamfanin a matsayin jagoran harkokin kasuwanci.
A jawabinsa, Shugaban Hukumar NASCON Allied Industries Plc da Mataimakin Shugaban Kamfanin Dangote Group, Olakunle Alake sun ce: “A matsayinmu na kamfani da aka ambata, muna da alhakin kula da masu hannun jari.
Mista Alake ya bayyana bayar da kyaututtukan a matsayin abin haɗin gwiwa, yana mai ƙara da cewa ba za a iya samun nasara a ware ba.
Sabuwar Daraktan Gudanarwa na Rukunin Kamfanin Matatar Man Fetur na Dangote Fatima Aliko Dangote, ta bayyana godiyarta ga abokan ciniki saboda jajircewarsu.
Manajan Darakta na NASCON Allied Industries Plc, Aderemi Saka, ya bayyana cewa an bada wadannan kyaututtukan domin yin murna da kuma yaba wa abokan cinikin kamfanin.
Da yake magana a madadin wadanda aka ba kyautar, Ali Balarabe, ya yaba wa Hukumar, gudanarwa, da ma’aikatan kamfanin.
Sauran da suka sami kyaututtukan sun haɗa da Alhaji Ibrahim Achida, Muabsa Integrated Services, Fanisau Enterprises, Idris Saleh Nigeria Limited, Sani Adamu Trader, da GIA Global Concept, da sauransu.