Kamfanin Glo ya bayar da kyautar kashi 200 ga abokanen huldarsa

Masu amfani da layin kamfanin Glo sun yi farin ciki yayin da kamfanin ya bullo da sababbin kyaututtuka don dadada wa abokanen huldarsa. Kyaututtukan sun hada da kyautar kashi 200 na lokacin kira da na shiga yanar gizo da kyautar da ake kira ‘Glo Bounce and Data Bundles’ da masu amfani da wayar Samsung galady […]

Kamfanin Glo ya bayar da kyautar kashi 200 ga abokanen huldarsa
Kamfanin Glo ya bayar da kyautar kashi 200 ga abokanen huldarsa

Masu amfani da layin kamfanin Glo sun yi farin ciki yayin da kamfanin ya bullo da sababbin kyaututtuka don dadada wa abokanen huldarsa.

Kyaututtukan sun hada da kyautar kashi 200 na lokacin kira da na shiga yanar gizo da kyautar da ake kira ‘Glo Bounce and Data Bundles’ da masu amfani da wayar Samsung galady S6 Edge da kuma masu amfani da wayar Samsung Galady S6 Flat.
Kamfanin ya bayyana sababbin kyaututtukan ne a wani taron manama labarai da ya gudanar a a harabar kamfanin da ke Legas a farkon makon nan.
Babban jami’in kasuwanci na shiyya, Ashok Israni ya bayyana cewa duk wanda ya sanya katin Glo na Naira 200 ko fiye da haka zai sami kyautar kashi 200 nan take.
Ya ci gaba da cewa ba kamar kyaututtukan kasuwa ba, wannan kyauta za a iya kiran kowane layi da ita a kwanaki bakwai na mako kuma za a iya kira tsarin ‘kai da iyalinka’ ba tare da wata matsala ba.
Ya bayyana cewa hakazalika mutum zai sami kyautar MB 15 na shiga yanar gizo tare da kyautar minti daya a kowane minti uku na kiran da mutum ya yi.
Amma a cewarsa, wanda ya shiga tsarin da ya sanya Naira 100 kacal, zai sami kyautar kashi 100 da kuma MB Data biyar na shiga yanar gizo.
Dangane da kyautar Glo Bounce kuwa, ya ce wannan tsari zai ba wanda yake amfani da shi damar shiga tsarin kira a kwabo 11 a kowace dakika.
To amma a cewarsa wannan tsari zai ba matasa masu yin amfani da layin Glo damar shiga a dama da su a harkar buga waya kamar ’yan makaranta da makamantansu.