Kamfanin Google Cloud zai bude ofishinsa na farko a Afirka
Zai taimaka wa abokanan hulda wajen watsa bayanansu ta yanar gizon.
A ranar Laraba ne kamfanin Google ya bayyana aniyarsa ta bude sabon ofishinsa na Google Cloud irinsa na farko a nahiyar Afirka.
Google wanda ya ce zai bude ofishin ne a Afirka ta Kudu, zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da kuma kara yawan abubuwan da suka shafi kasashen da ke yankin ta yanar gizo.
Sanarwar hakan dai ta bulla ne a taron da Kamfanin Google Cloud din ya gudanar karo na biyu a Jihar Legas.
Shi dai Google Cloud na daya daga cikin hanyoyin da Google din ke amfani da ita, wajen ba da jarin dala biliyan 1 ga al’umma, kamar yadda shugaban kamfanin Sundar Pichai ya yi alkawari a shekarar 2021.
Daraktan Kamfanin na Afirka Biral Patel, ya ce sabon shirin zai taimaka wa masu amfani da shi, hadi da masu sana’o’i da ke yankin wajen watsa bayanansu ta yanar gizon.
Patel ya ce baya ga haka, zai kuma inganta hanyoyin samun damammaki ga abokan ciniki da samar da ayyukan yi ga matasa.
Daraktan ya kuma ce tuni Google Cloud ya fara aiki tare da abokan huldarsa da ke nahiyar, tare da taimaka musu magance matsalolin kasuwanci masu tsauri, da ba su damar amfani da yanar gizo, domin cin gajiyar fa’idodin fasahar zamanin.
Nitin Gajria, Manajan Daraktan Google Africa ya ce akwai yiwuwar tattalin arziki ta yanar gizo ya bunkasa zuwa dala biliyan 180 nan da shekarar 2025, kwatankwacin kashi 5.2 na kudin shigar nahiyar.
Gajria ya ce Google na ci gaba da tallafa wa kananan kasuwancin Afirka ta tsarin Hustle Academy, da na Google Profiles Business.