Kamfanin Google ya karrama dalibin da fi tsufa a Kenya

A ranar Litinin da ta gabata ne kamfanin Matambayi ba ya bata na Google ya karrama dattijon nan dan kasar Kenya, wanda ya kasance dalibin firamaren da ya fi kowanne tsufa a kasar, kamar yadda littafin bajinta na Guiness World ya bayyana shi. Dattijon mai suna Kimani Maruge wanda ba shi da takadar haihuwa da […]

Kamfanin Google ya karrama dalibin da fi tsufa a Kenya
Kamfanin Google ya karrama dalibin da fi tsufa a Kenya

A ranar Litinin da ta gabata ne kamfanin Matambayi ba ya bata na Google ya karrama dattijon nan dan kasar Kenya, wanda ya kasance dalibin firamaren da ya fi kowanne tsufa a kasar, kamar yadda littafin bajinta na Guiness World ya bayyana shi.

Dattijon mai suna Kimani Maruge wanda ba shi da takadar haihuwa da za ta tabbatar da shekarunsa. Mista Maruge mai shekaru 84 yana daya daga cikin mambobin kungiyar bore ta Mau Mau wacce ta jagoranci yin bore ga Turawan mulkin mallakar kasar a shekarun 1950.Ya halarci makarantar firamaren Kapkenduiywo, inda a can ne ya zama shugaban dalibai.
A watan Satumbar shekarar 2005 ne, Mista Maruge ya fara shiga jirgin sama a rayuwarsa, lokacin da zai je birnin New York na kasar Amurka domin yin jawabi a gaban taron karni na Majalisar dinkin Duniya akan muhimmancin ilimin firamare.
Kuma bayan rikicin bayan zaben kasar na shekarar 2007, dattijon ya kaurace wa muhallinsa, inda daga nan ne ya fara rashin lafiyar da ya yi ajalinsa a shekarar 2009.
Manajan Sadarwan kamfanin Google ya bayyana marigayin da wani gwarzo a fannin neman ilimi da fitilarsa ta haske duniya kan yadda shekaru ba sa hana neman ilimi.