Kamfanin Habib Engineering ya jinjina wa gwamnatin Zamfara kan tsaro
Kamfanin Habib Engineering ya jinjina wa gwamnatin Jihar Zamfara kan yadda take bai wa ma’aikatan kamfanin kariya ta musamman, saboda matsalar da ake fama da ita ta barayin shanu da masu garkuwa da mutane.Shugaban kamfanin na jihohin Arewa maso Yammna, Mista Muhammed Siajan ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a […]
Kamfanin Habib Engineering ya jinjina wa gwamnatin Jihar Zamfara kan yadda take bai wa ma’aikatan kamfanin kariya ta musamman, saboda matsalar da ake fama da ita ta barayin shanu da masu garkuwa da mutane.
Shugaban kamfanin na jihohin Arewa maso Yammna, Mista Muhammed Siajan ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke garin Gusau.
Ya ce sakamakon kariyar da suke samu kamfanin ya samu nasarar kammala ayyukan da yake gudanarwa a wasu kananan hukumomin jihar.
Ya ce a kananan hukumomi 14 da ake da su daga 2011 zuwa 2015 sun samu nasarar kammala gina hanyoyi masu murabba’in kilomita 90 kan Naira biliyan, a fadin jihar.
Manajan ya ce hanyoyin sun kunshi hanyoyin cikin gari a hedikwatocin kananan hukumomin jihar 14 da kuma wasu sassan jihar, ya ce kamfaninsa ya kwashe shekara 16 yana gudanar da ayyukan raya kasa daban-daban a jihar.
Sai dai shugaban ya nemi al’ummar jihar su rika ba da goyon baya ga gwamnati wajen kulawa da ayyukan da aka yi masu, musamman abin da ya shafi kwalbatoci, wadanda jama’a da dama suke kokarin cike su da shara. Ya ce ya dace su zama masu kula da abin da gwamnati ta yi musu domin a cewarsa su ne masu amfana da su.