Kamfanin Hyundai ya hada gwiwa da na Truckmasters
Kamfanin motoci na Hyundai na Najeriya ya zabi kamfanin Truckmasters da ke sarrafa karafa a matsayin daya daga cikin manya dilolinsa. Kamfanin ya bayyana hakan ne a lokacin bikin cimma yarjejeniyar a Legas a ranakun karshen makon.Manajin-Daraktan Kamfanin Hyundai Motors Nigeria Limited da ke reshen Kamfanin Stallion Group Mista Parbir Singh ya ce kamfanin Truckmasters […]
Kamfanin motoci na Hyundai na Najeriya ya zabi kamfanin Truckmasters da ke sarrafa karafa a matsayin daya daga cikin manya dilolinsa.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a lokacin bikin cimma yarjejeniyar a Legas a ranakun karshen makon.
Manajin-Daraktan Kamfanin Hyundai Motors Nigeria Limited da ke reshen Kamfanin Stallion Group Mista Parbir Singh ya ce kamfanin Truckmasters zai taimaka wajen sayar musu da motocinsu da kuma samo musu masu saya a yankin Ikeja da Maryland da ma kasa gaba daya.