Kamfanin Konica Minolta ya sake kaddamar da sababbin na’urori
Kamfanin nan da ya yi fice wajen kera na’urorin dab’i mai suna Konica Minolta ya sake kaddamar da sababbin na’urorin dab’i daban-daban don amfanin manya da kananan ’yan kasuwa. An yi bikin kaddamar da sababbin na’urorin ne  Bizhub 215 da bizhub 165 da bizhub 363 da bizhub C554 da bizhub C25 da kuma bizhub C454.Ya […]
Kamfanin nan da ya yi fice wajen kera na’urorin dab’i mai suna Konica Minolta ya sake kaddamar da sababbin na’urorin dab’i daban-daban don amfanin manya da kananan ’yan kasuwa.
An yi bikin kaddamar da sababbin na’urorin ne  Bizhub 215 da bizhub 165 da bizhub 363 da bizhub C554 da bizhub C25 da kuma bizhub C454.
Ya bayyana cewa sababbin na’urorin suna da saukin sarrarafawa da kuma saukin gyarawa.
A ganinsa daya daga cikin garabasar da mutum zai samu idan ya sayi na’urorin shi ne za su taimaka masa wajen gudanar da ayyukansa daga ko’ina a duniya.
Ya kara da cewa daya daga cikin dalilan da ya sa na’urorin kamfanin Konica suka yi fice shi ne ba a samun cushewar takarda yayin da mutum yake aiki da su.
‘Ba kamar sauran na’urorin dab’i ba da ke samun tangardar cushewar takarda. Na’urorinmu na Konica Minolta ba sa samun wannan matsala saboda fasahar zamani da aka sanya musu. Shi ya sa ka ga na’urarmu ta C454 za ta yi maka dab’i a lokaci guda ta fitar da kala da sanya lambar shafi ta hada su wuri daya ta matsa da allura ta fitar maka da littafi cikin kankanin lokaci ba tare da wata wahala ba ko bata lokaci ba’. Inji shi.
Kamfanin ya baje kolin na’urori daban-daban manya da kanana sannan ya gabatar da takaitacciyar lacca kan yadda mutum zai yi kasuwanci da na’urorin kamfanin tare da samun riba mai yawa.