Kamfanin mai yana bayar da lita 2 kyauta ga wanda ya karanta Alkur’ani a Indonesiya

Wani kamfani fetur da iskar gas na kasar Indonesiya ya yi alkawarin bayar da litar mai biyu ga duk wanda ya karanta sura guda daga Alkur’ani.Kusan duk gidan man da masu ababen hawa suka yi layi, sai a nuna musu tallar kyautar mai ga duk wanda ya karanta Alkur’ani cikin watan Ramadan. Kamfanin man mallakar […]

Kamfanin mai yana bayar da lita 2 kyauta ga wanda ya karanta Alkur’ani a Indonesiya
Kamfanin mai yana bayar da lita 2 kyauta ga wanda ya karanta Alkur’ani a Indonesiya

Wani kamfani fetur da iskar gas na kasar Indonesiya ya yi alkawarin bayar da litar mai biyu ga duk wanda ya karanta sura guda daga Alkur’ani.
Kusan duk gidan man da masu ababen hawa suka yi layi, sai a nuna musu tallar kyautar mai ga duk wanda ya karanta Alkur’ani cikin watan Ramadan. Kamfanin man mallakar gwamnati na Pertamina ya fito da wannan tsarin ne don bai wa mutane kwarin gwiwa su zama Musulmi nagari, ta hanyar karanta wata sura daga Alkur’ani.
Gidan man da ya himmatu wajen bayar da wannan garabasa, ya yi masallaci, kuma yana samun dimbiun masu ziyara.
Moetawakkir, wani mazaunin Jakarta babban birnin kasar, na daya daga cikin wadanda suka samu wannan garabasa a gidajen mai biyar. Ya sa ran sauke Alkur’ani nan da karshen watan Ramadan.
“Muyn san cewa, idan muka yi aikin kwarai za mu samu lada. Karanta Alkur’ani a kowace rana, zai ba mu damar saukewa nan da karshen wannan watan, gas hi kuma an cika mana tankin mu,” a cewar Moetawakkir , inda ya bayyana yadda ya yi karatun minti 30 a zuwansa gidan man karo na biyu.
Wadanda suka shiga wannan gasar karanta Alkur’ani don samun gwaggwabar ladar cika tankin mota, sai sun cika fom, sannan a shigar da su masallaci su yi karatun. Lita biyun da ake bayarwa kyauta ta isa ta cika tankin babur, wanda shi ne abin sufuri mafi yawa a kasar.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano