Kamfanin Media Trust ya horar da ɗaliban Jami’ar ABU kan aikin jarida
Naziru Mika’ilu ya ce wannan kokarin kamfanin ne na karfafa gwiwar ɗaliban kan sanin makamar aikin jarida
Kamfanin Media Trust, masu Jaridar Daily Trust da Aminiya da Gidan Talabijin da Rediyo na Trust, ya yi wa daliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya bita kan aikin jarida a aikace.
Kamfanin ya horar da ɗaliban yadda ake gudanar da aikin jarida a aikace tare da wayar da kansu game da hanyoyin samun gurbin aiki a kafofin yada labarai.
- Tsadar rayuwa: Garin kwaki ya kashe wata yarinya a Kano
- Roberto Mancini ya zama sabon kocin Saudiyya
Taron horarwar da wayar da kai wadda aka gudanar a sashen dalibai masu karatun gaba da digiri na farko wato Post Graduate na Jami’ar ABU, ya samu halartar ɗalibai da malaman sashen nazarin aikin jarida na jami’ar.
Babban Darakta kuma Babban Editan Labarai da Harkokin Intanet na kamfanin, Naziru Mika’ilu Abubakar ya ce wannan yunkuri daya ne daga cikin kokarin kamfanin na karfafa gwiwar ɗaliban kan sanin makamar aikin jarida da nuna masu damar da suke da ita wajen zama manyan ’yan jarida a nan gaba.
Ya bayyana cewa Kamfanin Media Trust na inganta kwazon dalibai a matsayinsa na daya daga cikin manyan kafofin yada labarai sahihai da ya shahara wajen fadada ayyukansa.
Naziru Mika’ilu ya ce yanzu haka, kamfanin yana da sashen Turanci wato Daily Trust, sai sashen Hausa na Aminiya ta Hausa, sashen Talabijin da kuma Rediyo, baya ga sashen isar da sakon gaggawa na Online, wato ta intanet.
Ya ci gaba da cewa wannan yunkuri na horar da dalibai kudiri ne na Majalaisar Gudanarwar Kamfanin wanda za a ci gaba da yi a manyan makarantu da jami’o’i a fadin ƙasar nan.
Babban Editan ya ce “wannan wani nauyi ne da kamfanin ya daukar wa kansa don habaka kwazon dalibai tare da nuna masu muhimmanci da darajar aikin jarida a rayuwar al’umma.”
Ya kuma sanar da dalibai cewa akwai damarmaki ta samun aiki gare su musamman ma idan suka dage suka yi kokarin da ya dace a karatunsu.
Ita ma Shugabar Sashen Kula da Walwala da Bunkasar Ma’aikata ta kamfanin, Dokta Hadiza Bala ta ce tun da dadewa, Kamfanin Media Trust na ba da damar daukar aiki ga daliban da suka fita kyakkyawan sakamako (First Class) a fannin aikin jarida.
Ta kuma kwadaita masu cewa, ba sai kawai ɗaliban da suka fita da sakamakon mai daraja da farko ba, har da wadanda suka jajirce tare da yin kwazo musamman a bangaren sarrafa kwamfuta suna samun damar aiki da kamfanin.
Da yake nuna farin cikinsa, Babban Shugaban Tsangayar Ilmin da ya Shafi Al’umma, Shamsuddeen Mohammed ya yi fatar irin wannan hadin gwiwa zai ci gaba.
Ita ma Shugabar Sashen Nazarin Aikin Jarida, Adama Adamu ta yaba wa kamfanin bisa daukar nauyin gudanar da horon, inda ta ce dalibai sun karu sosai bisa koyarwar da aka yi masu.
Ta yaba wa Kamfanin Media Trust bisa kasancewarsa gidan jarida da ya shahara wajen buga ingantattun labarai da kuma bai wa kowa dama kafin buga labaransu.
Daliban sashen sun mika wa Babban Editan kwafin jaridun da dalibai ’yan ajin karshe na sashen suka buga tare da wallafawa.