Kamfanin Media Trust ya kafa kwamitin masana tattalin arziki

Kamfanin Media Trust Limited, mai buga jaridun Trust da Aminiya ya kaddamar da kwamitin masana tattalin arziki.Kwamitin ne zai jagoranta tare da nazarta jaridun kamfanin kan harkokin kudi da harkokin kasuwanci da suka shafi da kuma tattalin arzikin duniya.Da yake jawabi a wurin kaddamar da kwamitin a ranar Asabar da ta gabata, Babban Editan Kamfannin, […]

Kamfanin Media Trust ya kafa kwamitin masana tattalin arziki
Kamfanin Media Trust ya kafa kwamitin masana tattalin arziki

Kamfanin Media Trust Limited, mai buga jaridun Trust da Aminiya ya kaddamar da kwamitin masana tattalin arziki.
Kwamitin ne zai jagoranta tare da nazarta jaridun kamfanin kan harkokin kudi da harkokin kasuwanci da suka shafi da kuma tattalin arzikin duniya.
Da yake jawabi a wurin kaddamar da kwamitin a ranar Asabar da ta gabata, Babban Editan Kamfannin, Malam Mannir dan-Ali ya ce kwamitin zai taimaka wajen gano yadda ya fi dacewa wajen karfafa bayar da labaran da suka shafi tattalin arziki a jaridun.
Ya ce kwamitin zai rika yin taro a kowane wata uku domin tattaunawa tare da bayar da shawarwari kan fasalin tattalin arziki da kuma halin da tattalin arzikin kasa da na duniya suke ciki.
Kwamitin yana karkashin shugabancin Farfesa Mike Kwanashie ne Shugaban Jami’ar
beritas Unibersity da ke Bwari, yayin da Mista Tope Fasua zai kasance sakatarensa.
Sauran wakilan kwamitin sun hada da Farfesa Ode Ojowu tsohon mai ba Shugaba Olusegu Obasanjo shawara kan Tattalin Arziki da Malam Sanusi Abubakar, wani masanin tattalin arziki kuma marubuci a jaridar Daily Trust da Dokta Muhammed Muttaka Usman, tsohon shugaba sashin tattalin arziki na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da Farfesa dalhatu Mohammed Galadanci na sashin tattalin arziki na Jami’ar Bayero, Kano.
Sauran su ne Manajan Daraktan Kamfanin Media Trust Limited, Alhaji Isiak A. Ajibola da Darakta a Kamfanin Media Trust Limited, Alhaji Hussaini Abdulrahaman da kuma Babban Editan Malam Mannir A. dan-Ali.
A jawabinsa Farfesa Kwanashie ya ce kwamitin zai taimaka wa jaridun Kamfanin Media Trust su tsallake batun bayar da adadi zuwa ga bayar da labarai tare da saukaka su domin fahimtar da makarantan su.