Kamfanin Media Trust ya samu sabon Babban Jami’in Gudanarwa

Hukumar Daraktocin Kamfanin Media Trust Limited (MTL), mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya ta sanar da nada Malam Mannir dan-Ali a a matsayin Babban Jami’in Gudanarwa na kamfanin, sakamakon ritayar da Malam Kabiru Yusuf zai yi daga mukamin a karshen watan nan na Disamba.Sanarwar nadi ta zo ne jim kadan da kammala taron daraktocin […]

Kamfanin Media Trust ya samu sabon Babban Jami’in Gudanarwa
Kamfanin Media Trust ya samu sabon Babban Jami’in Gudanarwa

Hukumar Daraktocin Kamfanin Media Trust Limited (MTL), mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya ta sanar da nada Malam Mannir dan-Ali a a matsayin Babban Jami’in Gudanarwa na kamfanin, sakamakon ritayar da Malam Kabiru Yusuf zai yi daga mukamin a karshen watan nan na Disamba.
Sanarwar nadi ta zo ne jim kadan da kammala taron daraktocin da ya gudana a Abuja, makon jiya.
Kafin sabon mukamin nasa, sabon Babban Jami’in ya kasance Daraktan Gudanarwa kuma Babban Editan  jaridun kamfanin tun daga shekarar 2007. Malam Mannir ya samu digirin farko da na biyu a Ingilishi a Jami’ar Bayero Kano, kuma yana da kwarewa a aikin jarida na tsawon shekara 23 a matsayin dan rahoto, mai tsara shirya-shirye a rediyo da kuma edita. Ya gudanar da ayyukansa a Gidan Rediyon BBC da mujallar Citizen da kuma kamfanin Media Trust Limited.
Tunda ya fara aiki da kamfanin, shekara takwas da suka gabata, Mannir dan-Ali ya jajirce wajen inganta jaridun kamfanin, har ma da bangaren intanet da ake wallafawa. Shi dai wannan sabon mukami, zai gudana ne na tsawon shekara biyu, inda zai fara daga ranar 1 ga Janairun badi.
Sabon Babban Jami’in Gudanarwar, zai yi aiki ne tare da wasu jami’ai da suka hada da, Mista Abhay Desai, a matsayin Babban Jami’in Tafiyarwa, wanda a farkon bana ne ya kama aiki da kamfanin da sauran daraktoci biyu da za su shugabanci bangaren jarida da kuma kasuwanci, wato Mahmud Jega da Aliu Akoshile, tare da sauran manyan manajojin kamfanin.
A nasa bangaren, Babban Jami’in Gudanarwa mai barin gado, Malam Kabiru Yusuf, wanda shi ne tare da wasu suka kafa kamfanin a 1996, zai ci gaba da rike mukamin Shugaban Daraktocin Kamfanin. Ya kasance masani sosai a harkar jarida da rediyo, domin kuwa ya kwashe sama da shekara 30 a harkar.
Ya yi karatunsa na jami’a ne a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya da Jami’ar Toronto da ke kasar Canada, inda ya samu digiri na farko da na biyu a ilimin Kimiyyar Siyasa. Ya koyar a Jami’ar Sakkwato, kafin a canja mata suna zuwa Jami’ar danfodiyo; kafin ya tsunduma cikin aikin jarida, aikin da ya kasance cikinsa har zuwa yanzu.
A matsayinsa na wanda ya kawo tunanin kafa kamfanin tare da mutane kalilan, Malam Kabiru ya samu nasara, musamman ganin yadda Allah Ya albarkaci kamfanin, wanda da farko mazauninsa ke Kaduna, har ta kai ya dawo Abuja. A halin yanzu akwai ma’aikata sama da 500 da ke aiki a karkashinsa. Kuma an gina katafaren gini mai hawa biyar a matsayin cibiyar kamfanin ta dindindin, kamar kuma yadda kamfanin ya kasance mamallakin na’urorin buga jaridu na kashin kansa a Kano da Maiduguri da Legas.
Shugaban ya yi namijin kokarin kafawa da bunkasa kamfanin jaridar mai kima da daraja a idon jama’a, wanda kuma ake darajawa a duk fadin kasar nan. Jaridun kamfanin dai suna fitowa kowace rana, babu fashi, har ma da karin jaridar Hausa ta Aminiya da ke fitowa kowace Juma’a, tare kuma da mujallar shekara-shekara ta Kilimanjaro.
A yayin da yake aje mukamin Babban Jami’in Gudanarwa na kamfanin, Malam Kabiru Yusuf zai ci gaba da kasancewa Mataimakin Shugaban kungiyar Mawallafa Jaridu ta Najeriya (NPAN), kamar kuma yadda zai ci gaba da kasancewa mamba na hukumar tafiyar da Makarantar Koyon Aikin Jarida ta Duniya da ke birnin bienna, kasar Austiriya (IPI).
Ajiye mukamin da Malam Kabir ya yi, na daya daga cikin tsare-tsaren bunkasa kamfanin da aka bullo da shi, wanda a bara ma Manajan Daraktan kamfanin na farko, Alhaji Isiak Ajibola ya yi ritaya. An maye gurbinsa da wani jami’in, wanda ba ya da hannun jari a kamfanin, wanda yake kwararre ne a fannoni da dama na harkar jarida, wato Abhay Desai.
Wadannan canje-canje za su ci gaba da wakana, inda nan gaba mamallakan hannun jari a kamfanin za su zare hannunsu, a maye makwafinsu da kwararrun manajoji domin tafiyar da kamfanin bisa inganci daidai da kowane kamfani irinsa a duniya.