Kamfanin Media Trust ya tallafa wa marayu dalibai 100 da Naira miliyan 10
Kimanin marayu 100 da suka fito daga kananan hukumomin da rikicin Boko Haram ya daidaita a Jihar Borno, kuma a yanzu suke zaman gudun Hijira tare da karatu Makarantar Future Probince School, da ke Maiduguri ne za su ci gajiyar tallafin Naira miliyan 10 da Kamfanin Media Trust, mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya […]
Kimanin marayu 100 da suka fito daga kananan hukumomin da rikicin Boko Haram ya daidaita a Jihar Borno, kuma a yanzu suke zaman gudun Hijira tare da karatu Makarantar Future Probince School, da ke Maiduguri ne za su ci gajiyar tallafin Naira miliyan 10 da Kamfanin Media Trust, mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya bayar don agaza wajen karatunsu.
Wasu daga cikin daliban da suka ci gajiyar tallafin sun nuna murna da farin cikinsu dangane da tallafi inda suka yaba wa Kamfanin Media Trust.
Wata marainiya mai suna Fanna Muhammad Ali, ta ce ta yi murna domin tallafin zai taimaka mata wajen karatunta, “Ka san an kashe mahaifina ba ni da wanda zai dauki nauyin karatuna shi ne da muka samu labarin wannan makaranta, na fara karatu a nan ga shi kuma wannan kamfani ya zo ya tallafa mana.
Gwargwado muna fahimtar karatunnamu, yanzu shekarata 15, a gaskiya na samu ilimin addini da na zamani, da samun wannan tallafi za mu ci gaba da kokarin neman ilimi,” inji ta.
Maryam Abba, wadda ta ce tana daya daga cikin daliban Makarantar Sakandaren Chibok da ’yan Boko Haram suka sace wasu dalibanta, ta ce Allah ne Ya yi mata gyadar dogo ta koma gida da wuri daga makarantar kafin a sace su. “A ranar da aka sace kawayena ina tare da har wajen karfe 6:00 na yamma, to amma na bar su a lokacin kuma washegari sai na samu labarin abin da ya faru da su da misalin karfe 10 na dare. A gaskiya na yi bakin ciki da faruwar al’amarin, domin mun fara zaman jarrabawar karshe ta fita ke nan aka sace kawayena, ba zan sake komawa Chibok da zama ba, saboda a can ban san ilimin addinina ba, to amma ka ga a yanzu ina iya karanta Alkur’ani da wasu littattafai ga kuma karatun zamani, saboda haka muna yi wa wannan makaranta da shugabanninta godiya, su ma wannan kamfani da suka kawo mana tallafi mun gode musu, Allah Ya saka musu da alheri,” inji ta.