Kamfanin Media Trust ya tallafa wa ’yan gudun hijira a Gombe
Gidauniyar Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar da hadin gwiwar kamfanin Media Trust Limited, mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya sun raba wa ’yan gudun hijira 1000 kayayyakin tallafi na kimanin Naira miliyan biyar a Jihar Gombe. Bikin ba da tallafin ya gudana ne a fadar Mai martaba Sarkin Gombe, wanda ya samu halartar […]
Gidauniyar Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar da hadin gwiwar kamfanin Media Trust Limited, mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya sun raba wa ’yan gudun hijira 1000 kayayyakin tallafi na kimanin Naira miliyan biyar a Jihar Gombe.
Bikin ba da tallafin ya gudana ne a fadar Mai martaba Sarkin Gombe, wanda ya samu halartar manyan mutane da ’yan kasuwa da malaman addini da kungiyoyi masu zaman kansu da sauran jama’a daga sassan jihar.
Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar ya jinjina wa kamfanin buga jaridun Daily Trust da Aminiya kan kokarinsa na tallafa wa ’yan gudun hijirar da kuma kafa wata gidauniya don samar da tallafin. Ya ce kamfanin ya yi abin a yaba masa wajen tallafa wa marasa galihu da suke yi a fadin Najeriya. Sarkin ya kara da cewa, tallafa wa ’yan gudun hijira ba hakkin gwamnati kadai ba ne, hakki ne na dukkan ’yan Najeriya, domin duk wani dan Najeriya yana da gudunmawar da zai bayar wajen ba da tasa gudumawar. Daga nan sai ya bayyana muhimmancin taimaka wa ’yan gudun hijira sannan ya yi kira ga al’umma cewa su yi koyi da kamfanin Media Trust.
A jawabin Mataimakin Babban Manaja mai kula da sashin sadarwa na kamfanin Media Trust, Injiniya Garba Aliyu, ya ce batun bullo da yadda za a taimaki ’yan gudun hijirar, daraktocion kamfanin ne suka bullo da shi, wanda yana daga cikin tsarin kamfanin na ta taimaki ’yan gudun hijira.
Ya ce kamfanin yana ba da tallafin karo karatu ga dalibai da kuma gudanar da aikace-aikace da suka shafi inganta rayuwar dan Adam. Haka kuma kamfanin na Media Trust ya alakanta kansa ne da gidauniyar ta Sarkin Gombe saboda sadaukar da kai da kuma jajircewarta wajen gudanar da aikace-aikace don gina kasa, sannan sai ya jinjina wa sarkin bisa kafa wannan gidauniya tasa.
Malam Abdullahi Abubakar Lamido, malami a Jami’ar Bayero Kano, jinjina wa sarkin ya yi wajen daukar nauyin karatun yara kanana ’yan firamare da sakandare guda 1,500, sannan yana raba kayayyakin masarufi a lokutan azumi da sutura ga ’ya’yan marasa galihu, sai ya roki jama’a su yi koyi da kamfanin jaridar Media Trust.
A jawabansu daban-daban a madadin wadanda suka ci gajiyar, Adamu Kalabata da Hadiza Abba, yaba wa kamfanin Media Trust da Sarkin Gombe suka yi bisa wannan tallafi da ake ba su, sannan suka yi addu’ar Allah
Ya saka musu da gwaggwabar lada.