Kamfanin Media Trust ya yi taro da wakilansa

Babban Edita kuma Babban Jami’in Gudanarwar Kamfanin Media Trust Limited mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya, Malam Mannir Dan-Ali ya bukaci ’yan jarida da suke aiki da kamfanin su rike gaskiya da amana tare da sanin ya kamata a yayin gudanar da aikinsu domin ciyar da kamfanin gaba. Malam Mannir Dan-Ali ya bayyana haka […]

Kamfanin Media Trust ya yi taro da wakilansa

Babban Edita kuma Babban Jami’in Gudanarwar Kamfanin Media Trust Limited mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya, Malam Mannir Dan-Ali ya bukaci ’yan jarida da suke aiki da kamfanin su rike gaskiya da amana tare da sanin ya kamata a yayin gudanar da aikinsu domin ciyar da kamfanin gaba.

Malam Mannir Dan-Ali ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen taron  shekara-shekara na ma’aikatan sashin labarai da kamfanin ya shirya wa editoci da masu dauko rahoto don kara inganta labaran da jaridun kamfanin suke bugawa wanda aka gudanar a Abuja.

Babban Jami’in Gudanarwar  kamfanin ya ce lura da yadda zabubbukan badi suke kara karatowa, dole dukan masu dauko rahoto a fadin kasar nan su daura damara dauko rahoto ba tare da nuna bambanci ko alaka da wata jam’iyya ba.

Sannan ya hori ’yan jarida su tabbatar sun dauko cikakken bayani kuma na gaskiya, ta hanyar bin diddigin labaran da suka dauko tare da jin ta bakin kowane bangare kafin buga labari. Shugaban ya yi kashedin cewa kamfanin ba zai lamunci nuna rashin kwarewa a aiki ko nuna bangaranci ba.

Sai ya umarci ma’aikatan kan su dage  wajen dauko labaran binciken kwakwaf da kuma manyan labarai, ba kawai kananan labarai da kuma bayanan da ma’aikatu ko hukumomi ke fitarwa ba.

Mataimakin Babban Editan, Malam Mahmud Jega wanda ya gabatar da mukala kan dauko rahoton zabe, ya ce ya kamata kowane dan jarida ya mayar da hankali a kan tabbatar da abin da zai ruwaito, maimakon hanzarin yada labari ba tare da cikakken bincike ba, idan har ana so kamfanin ya ci gaba da zama yardajje musamman a wannan lokaci na kafafen sadarwa na zamani na Intanet ke barazana ga aikin jarida.

Kuma ya bukaci ’yan jarida su tabbatar da gaskiya da kuma jin dukan bangarori da kuma yin taka-tsantsan da bin wadansu ’yan siyasa a hankali wadanda ka iya haddasa matsala don cimma bukatunsa.

Da yake jawabi a wajen, Editan Aminiya, Malam Salihu Makera ya yi kira ga sauran ma’aikatan kamfanin da su dauki kansu a matsayin ma’aikatan kamfanin baki daya, ta hanyar turo wa Aminiya labarai kamar yadda suke tura wa takwararta ta Ingilishi wato Daily Trust, ba su bar ma’aikatan bangaren Aminiya da kawai ba. Ya kara da cewa akwai labarai masu yawa wuraren da Hausawa suke zaune a sassan Kudancin kasar inda akasari babu wakilan Aminiya, don haka ya bukaci wakilan kamfanin su rika dauko irin wadannan labaran su turo wa Aminiya koda kuwa da Ingilishi ne.

Taron wanda ya gudana a dakin taro na otel din Chida Hotel da ke Utako, Abuja, ya samu halartar dukan wakilan kamfanin Daily Trust da ke fadin Najeriya, inda aka tattauna yadda za a ciyar da kamfanin gaba.

Gabanin taron, Babban Jami’in Gudanarwar ya yi ganawa ta musamman da wakilan Aminiya a Hedkwatar Kamfanin Media Trust, inda ya nuna jin dadinsa kan yadda suke gudanar da ayyukansu, sannan ya bukaci su kara himma da jajircewa don bunkasa jaridar ta hanyar samar da ingantattun labarai tare da samar mata da kudin shiga.