Kamfanin Midamar ya shafe shekaru yana sayar wa Musulmi naman halal din bogi

Wani mai safarar kayan abinci ya shafe shekaru yana sayar wa Musulmin duniya naman shanun da yankansa ya saba wa shari’a, a cewar mai gabatar da kara a Amurka, inda ya gabatar da laifin mai kamfanin Midamar Corp., da ke garin Cedar Rapids a Jihar Iowa. Wannan kamfnai na Midamar ya sayar da naman shanu […]

Kamfanin Midamar ya shafe shekaru yana sayar wa Musulmi naman halal din bogi
Kamfanin Midamar ya shafe shekaru yana sayar wa Musulmi naman halal din bogi

Wani mai safarar kayan abinci ya shafe shekaru yana sayar wa Musulmin duniya naman shanun da yankansa ya saba wa shari’a, a cewar mai gabatar da kara a Amurka, inda ya gabatar da laifin mai kamfanin Midamar Corp., da ke garin Cedar Rapids a Jihar Iowa.

Wannan kamfnai na Midamar ya sayar da naman shanu na kimanin Dala miliyan hudu da dubu 900 ga Musulmin Malesiya da Kuwait da Hadaddiyar daular Larabawa da sauran kasashen Musulmi, alhalin ka’idar da aka bi wajen sarrafa naman ba a yi yankan Musulunci ba, duk da cewa an lika wa naman alamar takardun da ke nuni da cewa naman halal ne. An dai gabatar da karar daraktocin kamfanin a ranar 5 ga Disambar bana a gaban alkalai.
Kamfanin Midamar da daraktocinsa, wadanda ’yan uwan juna ne, su n hada da Jalel da William, wanda aka suaya wa suna zuwa “Yahya” Aossey, ana tuhumarsu da kulla makirci, da rubuta karya a jikin naman da suke sayarwa. Sannan ana kama wani kamfanin, wadannan ’yan uwa,. Mai suna Islamic Serbices of America da laifi, duk da cewa shi ne kamfanin da ya samu shaidar amincewar kasashen Malesiya da Indonesiya da Kuwait da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) wajen tantance naman shanun da ake safararsa zuwa kasashen. Wadanda ake zargi da aikata wannan laifi, ana tuhumarsu da aikata laifuka 91, wadanda suka ahda da rubutun karya da bayar da shaidar karya da zamba cikin aminci.
Wanda ya kafa kamfanin Midamar, William Aossey dan shekara 73 ya ki amsa laifukan da ake tuhumarsa da su. Sannan ’ya’yansa, ’yan shekara 40 da 44 an gabatar da su a babbar kotun Cedar Rapids.
Kamfanin Midamar ya bayar da sanarwar da ke nuni da cewa, wannan karakara keta hadi ne ga Kundin tsarin mulkin Amurka, wand aya bambanta tsakanin da Coci da hukuma, don haka ba daidai ba ne gwamnati ta yi hukunci kana bin da ya shafi yadda ake sarrafa abincin halal. Kamfanin ya yi nuni da cewam, ya shafe shekara 40, inda masu bincike ke bin kadin yadda ake yanka dabbobi.
Kamfanin Islamic Serbices of America ya bayar da sanarwar cewa, “zarge-zarge da zakule-zakulen laifuka ba za su bari su nakasa ayyukan su ba.” Kmfanonin wdanda suke a wuri guda suna da ma’aikata har 80, don muke godiya ga abokan huldarmu, saboda irin taimakon da suke yi mana.
Zargin aikata laifuka da aka yi wa Midamar, kamfanin da ya fara hada-hadar sarrafa abincin halala a Amurka, da kuma Islamic Serbices of America, duk sun nuna cewa, shaidun da suka bayar na Hukumar Kula da Kayan Gona ta Amurka “USDA” akwai takaddama tsakanin kamafnin da jami’an sa’ido na hukumar.
A hakikanin gaskiya, wadanda ke sayar wa Midamar shanu tun daga shekarar 2007 zuwa 2010, kamfanin sarrafa nama ne na grin Windom da ke Jihar Minnesota, wanda ke amfani da na’urar jefe shanu har sai sun mutu,” a cewar tuhumar laifin da aka yi wa kamfanin. Kuma fanin ba shi da izinin safarar shanu zuwa kasashen Indonesiya da Malesiya, sannan babu Musulmi da ke da kwarewar yanka, kuma ba sa yin addu’a, ko “Tasmia.” Don haka tuhuma ta hau kansu.
A duk sa’adda naman Midamar ya iso garin Cedar Rapids, sai ma’aikatan kamfanin su cire alamar da ke nuni da cewa an yi amfani da sinadarin acetone wajen sarrafa naman. Kuma ana zargin ma’aikatan wannan kamfani da lika alamar karya da ke nuni da cewa naman ya fito ne da masana’antar nama ta Omaha, wadda ke da lasisin fitar da kayan abinci zuwa kasashen Indonesiya da Malesiya. Midamar dai na fama tuhumar aikata laifin boye hakikanin inda yake samo naman da yake fitarwa, sannan hukumar USDA ta Amurka ta ba su duk na bogi ne.
Syed Rasheeduddin Ahmed, Shugaban kungiyar Musulmi masu mu’amala da kayan masarufi, ya ce tuni Musulmi ke zargin cewa naman da ake samarwa ba shi da tabbacin kimarsa ta cika a matsayin naman halal.