Kamfanin motocin KIA zai fara hada motoci a Legas

Kamfanin motocin KIA da ake yi wa lakabi da KIA Motors Nigeria ya cika alkawarin da ya yi shekarar da ta gabata, inda ya kaddamar da katafariyar masana’antar hada motoci a Legas. Wata takardar sanarwa da kamfanin ya fitar a makon da muke ciki ta nuna cewa sabon wurin hada motocin zai rika samar da […]

Kamfanin motocin KIA zai fara hada motoci a Legas
Kamfanin motocin KIA zai fara hada motoci a Legas

Kamfanin motocin KIA da ake yi wa lakabi da KIA Motors Nigeria ya cika alkawarin da ya yi shekarar da ta gabata, inda ya kaddamar da katafariyar masana’antar hada motoci a Legas.

Wata takardar sanarwa da kamfanin ya fitar a makon da muke ciki ta nuna cewa sabon wurin hada motocin zai rika samar da motoci guda dubu 25 a shekara.
Sanarwar ta bayyana cewa Ministan Harkokin Kasuwanci, Mista Olusegun Aganga ya bayyana farin cikinsa da nasarar da kamfanin KIA ya samu na kammala sabon wurin hada motocin nasa.
Sanarwar ta ce Aganga ya yi furucin ne yayin da ya kai ziyara gani-da-ido sabuwar masana’artar hada motocin inda ya ce: “Na yi mutukar farin ciki kuma na yi mamakin ganin ci gaban da aka samu da kuma irin na’urorin zamanin da na gani a wannan wuri. Na ziyarci wuraren hada motoci daban-daban a duniya amma zan gaya muku cewa irin na’urorin zamani da na gani a wannan wurin masu inganci babu shakka wannan masana’artar hada motoci za ta yi gogayya da sauran takwarorinta a duniya.”
Shugaban kamfanin Mista Jacky Hathiramani ya ce: “kokarin kafa wurin hada motocin ya zo sakamakon bukatar bunkasa kasuwanci a Najeriya, ta yadda kasar za ta kasance jagora a harkar masana’antu a kasashen Afirka da duniya baki daya.”
Ya bayyana cewa masana’antar hada motocin ta dauki wadanda suka kammala karatun injiniya a jami’o’in Najeriya kuma zai ci gaba da sama wa ’yan kasar ayyukan yi.
Sanarwar ta hakaito babban jami’in kasuwanci na kamfanin KIA, Mista Sandeep Malhotra yana cewa: “Irin yadda kamafnin KIA ke kara bunkasa a tsakanin kamafnoni a Najeriya zai ci gaba da tsere wa tsara wajen samar da motocin zamani ga abokanen huldarsa.”
A bara kamfanin ya yi alkawarin kafa sabuwar masana’antar hada motocin KIA a Najeriya. Kamfanin ya kaddamar da sababbin motocin da ya yi musu lakabi ‘kirar Najeriya’ kamar motar KIA samfurin Kia Rio da Kia Cereto da Optima da Sorento da kuma Kia Soul.
Kamfanin ya yi alkawarin fara hada wadansu samfurin kamar KIA Sedans da sauran samfuran motocin daban-daban har zuwa karshen shekarar da muke ciki.