Kamfanin MTN ya ba wasu makarantu gudunmawar kayan aiki a Legas

Kamfanin MTN ya baiwa makarantu 2, makarantar Oriwu model junior/secondary da kuma makarantar Orewo junior/senior grammer da ke cikin  karamar  Hukumar  Ikorodu gudunmowar kujerin dalibai da na  malamai da  littafan rubutu  da kuma gwagwanayen tarkacen kayan lissafi (math set) da  riguna ruwan dalibai. Da take karbar kayayyakin, a madadin gwamnatin Jihar Legas, Kwamishinar Ilimi, Misis  […]

Kamfanin MTN ya ba wasu makarantu gudunmawar kayan aiki a Legas
Kamfanin MTN ya ba wasu makarantu gudunmawar kayan aiki a Legas

Kamfanin MTN ya baiwa makarantu 2, makarantar Oriwu model junior/secondary da kuma makarantar Orewo junior/senior grammer da ke cikin  karamar  Hukumar  Ikorodu gudunmowar kujerin dalibai da na  malamai da  littafan rubutu  da kuma gwagwanayen tarkacen kayan lissafi (math set) da  riguna ruwan dalibai.
Da take karbar kayayyakin, a madadin gwamnatin Jihar Legas, Kwamishinar Ilimi, Misis  Olayinka Oladunjaiye ta yi na’am da abubuwan alherin da kamfanin na MTN ya saba yi wa jihar, musamman  a fannin ilimi.
Kwamishinar  ta ce  ilimi  ya fi  karfin gwamnati ita kadai, muddin ana son ba da  wadataccen ilimi ga yara, akwai bukatar kamfanoni  masu zaman  kansu  da ma masu hannu da  shuni  su ba da  tallafinsu.
Da yake  jawabinsa  wajen  mika  kayayyakin, shugaban  kula  da  fannin  ilimi  na  kamfanin na MTN, Mista bictor Orie Ononogbu ya ce  wannan kadan  ne daga  cikin  abin da kamfanin ya yi  ko  kuma  zai ci  gaba  da yi wa  fannin ilimi  a  Jihar  Legas  da ma sauran jihohin Najeriya.
Ya ce  duk  mazaunin Jihar  Legas  yana  ganin abin da  gwamnati ke yi  a  fannin ilimi  da ma  sauran  fannonin rayuwa daban-daban  don haka  bai  dace  a bar  gwamnati da wannan aiki ita kadai ba.
Su dai  wadannan makarantun  sun samu  kujerin dalibai 200 ne kowannensu,  kana guda 20 na malamansu,  yayin da takardun rubutu da gwangwanayen kayan lissafi da  rigar  ruwa  na  daliba masu  yawan gaske, wadanda  aka kiyasta  kudinsu  ya kai Naira miliyan 10.