Kamfanin MTN ya taimaka wa ta’addanci a Najeriya – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gazawar kamfanin sadarwa na MTN na kasar Afirka ta Kudu wajen yanke wayoyin da ba a yi musu rajista ba ya taimaka wajen kashe dubban mutane da mayakan kungiyar Boko Haram suka rika yi.Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata lokacin da […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gazawar kamfanin sadarwa na MTN na kasar Afirka ta Kudu wajen yanke wayoyin da ba a yi musu rajista ba ya taimaka wajen kashe dubban mutane da mayakan kungiyar Boko Haram suka rika yi.
Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata lokacin da yake ganawa da manema labarai tare da Shugaban Afirka ta Kudu Mista Jacob Zuma, wanda ya kawo ziyara kasar nan ya ce, saboda wannan dalili ne Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) ya ci tarar kamafnin Dala biliyan biyar da miliyan 200 (Naira tiriliyan daya da biliyan 400). An rage tarar zuwa Naira biliyan 780 daga baya.
Shugaba Buhari ya ce abin bakin ciki ne yadda jan kafar da kamfanin MTN ya yi wajen amfani da wannan umarni ya ba ’yan ta’addar damar yin amfani da kafar sadarwarsa.
Ya ce “Damuwar Gwamnatin Tarayy ita ce batun tsaro ba tarar da aka ci MTN ba. Kun san ’yan ta’adda na amfani da layukan da ba a yi wa rijista ba, kuma a tsakanin shekarar 2009 zuwa yau kungiyar Boko Haram ta kashe mutane akalla dubu 10. Wannan ne ya sa Hukumar NCC ta nemi kamfanonin MTN da Glo da sauransu su yi rajistar layukan abokan huldarsu.”
Shugaba Buhari ya ce, “Abin takaici MTN ya yi muguwar jan kafa wanda hakan ya taimaka wajen kashe mutane. Kumja Hukumar NCC ta duba ka’idojinta ta ci tararsa.” Ya ce karar da kamfanin MTN ya shiga a kotu ce ta jawo tsaikon tattaunawar da ake yi ta kara rage kudin tarar.
Tunda farko Shugaba Jacob Zuma ya ce shi da Shugaba Buhari sun tattauna batun zaman lafiya da tsaro a yankin Afirka inda suka nuna damuwa kan barazanar da ayyukan ta’addanci da tsaurin ra’ayi suke yi ga Najeriya da sauran kasahen Afirka.
Ya ce shi da Buhari sun sanya hannu a kan yarjejeniyoyin kasuwanci fiye da 30 da suka shafi hadin kai a fannin kasuwanci da masana’antu da sufuri da makamashi da tsaro da samar da zaman lafiya da kuma shigi da fici. “Kuma mun umarci ministocinmu su gano hanyoyin hadin gwiwa wajen gudanar da ayyukan da za su yi tasiri wajen bunkasa sassan tare da inganta ji dadin rayuwa da tattalin arziki da samar da aikin yi ga jama’armu,” inji shi.
Shugaba Jacob Zuma ya kuma ce gwamnatinsa za ta tabbatar da an dawo da kudin da gwamnatin Afirka ta Kudu ta kwace a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan ga Najeriya.
Ya ce gwamnatocin Najeriya da Afirka ta Kudu suna hada hannu kan lamari kuma an shirya wasu matakai na kwato kudaden da aka sace daga Najeriya a kai kasar. Ya ce ana ta kokarin yin bincike don tabbatar da duk dukyar da aka kai Afirka ta Kudu daga Najeriya ta haramtacciyar hanya an dawo da su.