Kamfanin NNPC ya baiwa Kachikwu amsa

Kamfanin Mai na NNPC zai bayar da amsa kan zarge-zargen da Karamin Ministan Albarkatun Mai, Ibe Kachikwu ya yi a kan Babban Manajan Daraktan Kamfanin, Maikanti Baru a takardar da ya aikewa Shugaba Muhammadu Buhari. Wata majiya da ke kusa da kamfanin NNPC ta tsaigunta wa Aminiya cewa kamfanin NNPC din ya samu damar baiwa […]

Kamfanin NNPC ya baiwa Kachikwu amsa

Kamfanin Mai na NNPC zai bayar da amsa kan zarge-zargen da Karamin Ministan Albarkatun Mai, Ibe Kachikwu ya yi a kan Babban Manajan Daraktan Kamfanin, Maikanti Baru a takardar da ya aikewa Shugaba Muhammadu Buhari.
Wata majiya da ke kusa da kamfanin NNPC ta tsaigunta wa Aminiya cewa kamfanin NNPC din ya samu damar baiwa karamin ministan amsa kan zarge-zargen da ya yi.
A takardar da ya aike wa shugaban kasa, Kachikwu ya zargi shugaban kamfanin NNPC da rashin biyayya tare da bayar da kwangiloli Naira biliyan 25 ba tare da bin ka’ida ba.