Kamfanin NNPC ya musanta zargin da Kachikwu ya yi
Kamfanin Mai na NNPC ya mayar da martani ga zarge-zargen da Karamin Ministan Albarkatun Mai, Dokta Ibe Kachikwu ya yi wa Shugaban Kamfanin, Dokta Maikanti Baru. Martanin ya zo ne sakamakon ummarnin da Shugaba Buhari ya baiwa Babban Manajan Darktan kamfanin na kare zargin rashin bin ka’ida wajen bayar da kwangiloli da kuma rashin biyayya […]

Kamfanin Mai na NNPC ya mayar da martani ga zarge-zargen da Karamin Ministan Albarkatun Mai, Dokta Ibe Kachikwu ya yi wa Shugaban Kamfanin, Dokta Maikanti Baru.
Martanin ya zo ne sakamakon ummarnin da Shugaba Buhari ya baiwa Babban Manajan Darktan kamfanin na kare zargin rashin bin ka’ida wajen bayar da kwangiloli da kuma rashin biyayya da karaminin ministan ya yi.
A wata sanarwa da Mai Magana Da Yawun Kamfanin, Ndu Ughamadu ya fitar ta nuna cewa zarge-zargen da karamin ministan ya yi ba su da tushe bare makama.