Kamfanin Nokia zai sallami ma’aikata 14,000 saboda rashin ciniki
Kamfanin ya ce ya dauki matakin ne saboda cinikinsa ya ragu
Kamfanin wayoyi na Nokia ya ce zai sallami akalla mutum 14,000 daga cikin ma’aikatansa daga yanzu zuwa nan da shekaru uku masu zuwa.
Kamfanin, wanda ya sanar da hakan a ranar Alhamis, ya ce adadin ya kai kusan kaso 16 cikin 100 na ma’aikatan nasa, kuma zai yi haka ne saboda koma-bayan da yake fuskanta a bangaren samun riba.
- Tinubu ya janye nadin da ya yi wa matashi mai shekara 24 a shugabancin FERMA
- Kotun Koli ta sanya ranar sauraron karar Atiku kan nasarar Tinubu
Kamfanin dai yana da ma’aikata 86,000, kuma ya ce wannan sallamar ma’aikatan zai sa ya rage kudaden da yake kashewa da kimanin Dalar Amurka biliyan 1.3.
Sanarwar ta kuma ce kamfanin ya fuskanci raguwar ciniki da kimanin kaso 20 cikin 100 da kuma raguwar ribarsa da kaso 69 cikin 100 daga watan Yuli zuwa Satumban da ya gabata, idan aka kwatanta da cinikin shekarar da ta gabata.
Wayoyin Nokia dai a baya sun taba zama ja-gaba a tsakanin kamfanonin wayoyi, amma daga bisani sun koma baya, lokacin da kamfanin Apple ya fara fitar da wayoyinsa samfurin iPhone a sheraka ta 2007.
Daga bisani kamfanin ya sayar da bangarensa na wayoyin salula ga kamfanin Microsoft a 2013.
Tun daga nan ne ya fi mayar da hankalinsa waje sayar da wasu kayayyakin na sadarwa da ba wayar salula ba.
Kamfanin na Nokia dai ba shi ne farau ba wajen daukar matakin rage yawan ma’aikatansa a ’yan kwanakin nan a tsakanin manyan kamfanonin sadarwa na duniya.